Uncategorized
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 1 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 1 ga Watan Afrilu, 2019
1. Hukumar EFCC na shirin daukan mataki akan Gwamna Amosun, Okorocha da Yari
Hukumar Bincike da Yaki kan Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta kafa wata rukuni da zata yi bincike akan wasu gwamnoni da ake zargi da kadamar da halin cin hanci da rashawa wajen hidimar zaben 2019.
Hukumar ta gabatar da cewa zata yi hakan ne kamin ranar rantsar da sabbin shugabannan kasa a ranar 29 ga watan Mayu a shekarar 2019.
2. Jam’iyyar PDP sun gabatar da sabuwar kara game da zaben Jihar Gwamnoni ta Jihar Katsina
Dan takaran kujerar Gwamna ta Jihar Katsina daga Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP), Yakubu Lado ya gabatar da sabuwar kara a gaban kotun kara kan hidimar zaben Gwamnoni da aka yi a baya.
Naija News ta gane da cewa dan takaran ya gabatar da karar ne bisa zaben gwamnoni da aka yi a ranar 9 ga watan Maris da ya gabata.
3. Lokacin da Shugaban Alkalan kasar Najeriya, CJN Tanko zai sauka daga shugabanci ya gabato
Watakila a fuskanci ‘yan matsalolin kadan a yayin da ya saura mako ukku da shugaban alkalan kasar Najeriya, Muhammad Tanko da shugaba Muhammadu Buhari ya sanya zai sauka daga matsayin.
Ka tuna da cewa shugaba Muhammadu Buhari a ranar 25, ga watan Janairu 2019, ya sanya Tanko a matsayin shugaban Alkalan kasar bayan da aka dakatar da tsohon shugaba, Walter Onnoghen.
4. Oshiomhole ya Murabus da hada kai da Jam’iyyar AAC
Ciyaman na Jam’iyyar APC ta tarayya, Adams Oshiomhole, ya gabatar da janye kansa daga duk wata hidima na Jam’iyyar AAC akan hidimar zaben Gwamnonin Jihar Rivers.
Oshiomhole yayi hakan ne da guje wa zargi da ake yi da shi na cewar jam’iyyar su na taimaka wa Jam’iyyar AAC don lashe zaben Jihar Rivers.
5. An gabatar da Gbajabiamila a matsayin Kakakin Gidan Majalisar Wakilai
A ranar Lahadi da ta gabata, an gabatar da Hon. Femi Gbajabiamila daga Jam’iyyar APC ta Legas a matsayin sabon Kakakin Yada Yawun Gidan Majalisa.
“Ina da shiri ta musanman na ganin cewa na kadamar da zumunci a kasar nan tamu” inji Gbajabiamila a yayin da yake bayani a gaban ‘yan gidan Majalisar.
6. Oshiomhole makaryaci ne – inji Marafa
Sanata Kabiru Marafa dake wakilcin Jihar Zamfara ta tsaka daga jam’iyyar APC, ya kalubalanci Ciyaman na Jam’iyyar APC ta tarayya, Adams Oshiomhole da fadin gaskiya game da jam’iyyar, musanman ga hidimar zaben firamare da jam’iyyar ta yi a watan Aktoba da ya gabata a shekarar 2018.
7. Ndume ba zai janye wa Lawan daga kujerar shugabanci ba
Wata rukunin masu ruwa da tsaki a Jihar Borno sun yi barazanar cewa tsohon shugaban Sanatocin kasar Najeriya, Sanata Muhammad Ali Ndume ba zai janye wa tseren zaman sabon shugaban gidan Majalisar Dattijai ba.
Naija News na da sanin cewa Shugaba Muhammadu Buhari, Jam’iyyar APC da wasu ‘yan gidan majalisar sun bada goyon baya ga Sanata Ahmed Lawan da zaman sabon shugaban Gidan Majalisar.
8. Mugun hadarin mota ya dauke rayuka 13 a Bauchi
Kimanin mutane goma sha ukku suka rasa rayukar su a wata mugun hadarin mota da ya auku a ranar Lahadi da ta gabata a kusa da kauyan Bishi.
Abin ya faru ne a yayin da wata Motar Bas ke kan hanyar Bauchi zuwa Gombe a ranar Lahadi da ta gabata.
Ka samu cikakken labarun kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa