Connect with us

Uncategorized

Mutane Goma Sha Ukku (13) sun mutu a wata Mumunar Hadarin Mota

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar 31 ga Watan Maris 2019, watau Lahadi da ta gabata, anyi wata hadarin mota da ya dauke kimanin rayuka 13.

Hadarin ya faru ne da tsakar ranar Lahadin a yayin da wata motar bas da ke dauke da mutane 13 hade da direban suka kahe da hadari a kusa da wata kauye da ake cewa Bishi, a hanyar da ta bi daga Bauchi zuwa Gombe.

Motar ta hade ne da wata mota a anan kan hanyar, har mutane 13 suka mutu sakamakon hadarin.

Abin takaici, wani Magidanji da Matansa da kuma yaran su biyu hade da wata ‘yar uwan su na cikin motar kuma sun mutu nan take,

An bayyana ga manema labarai da cewa Wannan magidanci da Iyalin sa na daga wani gidan sarauta ne da ake cewa ‘Yarin Bauchi.’

Zainab Sabitu, daya daga cikin ‘yan uwan Magidancin da matarsa, ta bayyana sunan mutumin da matar da kuma yaransu; “Mutumin sunashi Jamal Ahmed Yari, Matar kuma Amina, Yaran nasu guda biyu kuma Adnan da Affan, ita ‘yar uwan tasu kuma Zahra’u Dogo.” inji bayanin Zainab ga manema labarai.

Zainab ta kara bada tabbacin cewa lallai mugun hadarin ya faru tsakanin motoci biyun a hanyar Bauchi zuwa Gombe.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa wata ‘Yar Macce ta mutu a hadarin mota a yayin da take kan hanyar zuwa wajen hidimar bautan kasa (NYSC).