Connect with us

Uncategorized

‘Yan Hari da Bindiga sun kashe kimanin Mutane fiye 13 a Jihar Zamfara

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mahara da Bindiga sun kai wata sabuwar hari a kauyuka biyu ta karamar hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara ranar Lahadi da ta gabata.

Naija News Hausa ta gane da cewa kusan mutane goma sha shidda ne ‘yan harin suka kashe a kauyan Kursasa da Kurya a nan karamar hukumar Shinkafi, Zamfara.

Usman Garba, wani mazaunin kauyan Kursasa, ya gabatar ga manema labarai da cewa ‘yan harin sun fada wa kauyukan ne a missalin karfe goma (10PM) na daren ranar Lahadi, 31 ga watan Maris 2019 da ya gabata.

Ya bayyana da cewa ‘yan harin sun shigo ne kauyan da mugayan makamai da bindigogi.

“An take suka kashe mutane 9 a nan kauyan Kurkusa da kuma yi wa mutane da dama raunuka da harsasun bindiga” inji Usman.

“Bayan da kuma suka gama da kauyan Kurkusa, sai suka kara gaba zuwa kauyan Kurya inda suka kashe kimanin mutane bakwai a nan take, hade ma da ‘yan banga da suka fito don ganawar wuta da su”

Usman ya kara bayar da cewa da abin yayi zafi ‘yan bangan shiyar Kansas da kuma Kurya sun hada kai da ganawar wuta da ‘yan ta’addan kuma sun samu kashe daya daga cikin ‘yan harin.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa ‘Yan Hari da bindiga sun hari shiyar Rigasa ta Jihar Kaduna a ranar Alhamis 28 ga watan Maris 2019 da ta gabata, Inda suka kashe wani mutum da kuma sace matarsa.

‘Yan ta’addan sun fada wa yankin Rigasa da hari ne, suka kuma kashe Malam Abdul’azeez bayan nan suka sace matar tasa kuma. kamar yadda aka baiwa manema labarai.

Usman, a cikin bayanin sa ya bukaci hukumomin tsaro da su taimaka masu da tsaro ta gaske don magance matsalar mahara a yankin su.

Ko da shike an bayyana da cewa Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin watsar da Rundunar Tsaron kasa a dukan yankin Zamfara da ‘yan hari da makami ke kai wa farmaki.