Uncategorized
APC tayi sabuwar rashi: Alhaji Faruku da Matarsa Hajiya Nasara sun kone kurmus da wuta
Naija News Hausa ta samu sabon rahoto da cewa Jigon Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi, Alhaji Faruku Umar Dan Tabuzuwa da Matarsa, Hajiya Nasara Faruku sun kone har ga mutuwa sakamakon Gobarar wuta.
An gabatar ne ga manema labarai da cewa abin ya faru ne a ranar Lahadi da ta gabata a nan Birnin Kebbi.
Ko da shike ba a bada cikkaken bayani akan sanadiyar gobarar wutan ba, amma mun samu sani da cewa wutar ya kame ne da Alhaji Faruku da Uwargidan sa, Hajiya Nasara. Bisa bincike, an gane da cewa Hajiya Nasara babban sakatare ne na Hidimar Fensho na ma’aikatan makarantar Firamaren Jihar Kebbi.
Anyi wa Marigayi Faruku da Marigayia Nasara addu’ar karshe daga bakin Limamin Masallacin Jumma’ar Sarkin Gwandu, an kuma bizne su bisa dokar Islam.
Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa Matan Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu ta bayar da tallafi na kudi kimanin Naira Miliyan N2m ga mutane goma da ke dauke da ciwon Kanser a Jihar.
“Yaki da ciwon kanser a Jihar Kebbi abu ne mai muhimanci ga gwamnatin Jihar da kuma masu kudi da jari a Jihar, don ganin cewa an taimaka ga wadanda ke kame da wannan ciwo da kuma tabbatar da magance ciwon.” inji Dakta Zainab a yayin da take bayani wajen hidimar.