Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 2 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 2 ga Watan Afrilu, 2019

1. Hukumar INEC ta cigaba da kirgan Zaben Jihar Rivers

Hukumar Kadamar da Zaben Kasa, INEC a yau ta ci gaba da hidimar kirgan zaben Gwamnonin Jihar Rivers.

Naija News na da sanin cewa hukumar ta dakatar da hidimar zaben Jihar tun ranar 10 ga watan Maris 2019 akan wasu matsaloli da aka samu a wasu runfunar zabe a Jihar.

2. Ya Kamata ‘yan Gidan Majalisa su zabi shugabansu da kansu – inji Saraki

Shugaban Sanatocin Najeriya, Bukola Saraki ya shawarci Manyan shugabannan jam’iyoyi da janye kansu daga hidimar zaben wanda zai jagoranci gidan Majalisar Dattijai ta tara.

Ko da shike Saraki bai bayyana kowace jam’iya yake nufi ba, amma masu kula na zargin cewa watakila da shugabannan Jam’iyyar APC ya ke, saboda su ke kan mulki.

3. Shugabancin Kasa tayi magana game da Kisan Kolade Johnson

Shugabancin kasar Najeriya ta gabatar da gaisuwa ta musanman ga Iyali da Abokannan Kolade Johnson da hukumar SARS suka harbe da bindiga a Jihar Legas.

Naija News ta gane da cewa Hukumar SARS sun kashe Kolade ne a yayin da suka shiga zagaye a shiyar Mangoro/Onipetesi ta Jihar Legas don bincike da masu sanya kaya da shiri irin ta mashaya da ‘yan iska.

4. Sanata Saraki ya Lisafta Ayukan ci gaba da Majalisa tayi a shugabancin shi

A ranar Litini da ta gabata, shugabana Sanatocin Najeriya, Sanata Bukola Saraki, ya gabatar da wasu Ayukan ci gaba da Gidan Majalisar Dattijai ta kawo ga kasar a yayin da yake kan shugabancin gidan Majalisar.

Saraki ya gabatar da nasarar ne a yayin da yake bayani da sabbin ‘yan Majalisar da aka zaba ga zaben 2019.

5. Dalilin da ya sa na ziyarci shugaba Buhari – Okorocha

Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, ya gabatar da cewa ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari ne don ganyatar shugaban da zuwa Jihar Imo wajen Sanya hannu ga ayuka da ya kadamar a Jihar.

Mun tuna a Naija News Hausa a baya da cewa Hukumar INEC taki bayar da takardan komawa ga kan shugabanci a matsayin Sanata ga Okorocha, kamar yadda aka baiwa sauran Sanatocin kasar.

6. Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya sun gabatar da kame dan Sandan da ya kashe Kolade Johnson

Kwamishanan Hukumar Jami’an ‘Yan Sandan Jihar Legas, CP Zubairu Muazu ya bada tabbacin cewa sun kame rukunin ‘yan sanda da suka aiwatar da kisan Mista Kolade Johnson.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne a wata sanarwa da aka gabatar daga kakin yada labarai ga ‘yan sandan Jihar, DSP Bala Elkana.

7. Sojoji Najeriya sun ci karo da inda ake Kirar Bindigogi

Hedkwatan Rundunar Sojojin Najeriya ta ‘Operation Whirl Stroke’ (OPWS), a wata zagayen bincike da suka yi a Jihar Nasarawa, Taraba da Jihar Benue, sun gabatar da cewa sun ci karo da wasu mutane biyu da ake zargin su da kirar bindigogi a karamar hukumar Logo ta Jihar Benue.

Naija News Hausa ta samu gane da wannan labarin ne kamar yadda Maj-Gen Adeyemi Yekini, Kwamandan Rundunar Sojojin OPWS ya gabatar a garin Makurdi ga menama labarai a ranar Litini da ta gabata.

 

Ka samu cikkaken bayanin akan labarun kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa