Connect with us

Uncategorized

Wuta ya kone Mutane biyu har ga Mutuwa a wata hadarin Motar Tanki

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Talata, 2 ga watan Afrilu, A killa mutane biyu sun kone da wuta kurmus a wata hadarin Motar Tanki da ke dauke da Man Fetur a babban hanyar da ta bi Bauchi zuwa Jos.

Naija News Hausa ta samu rahoton ne da cewa hadarin ya faru ne a yayin da wata Motar Hilux ta ci karo da Motar Tanki da ke dauke cikke da Man Fetur, a nan take kuma suka kame da wuta.

Kakakin yada labarai ga Hukumar Kulawa da Tafiye-tafiye da aka fi sani da suna (Federal Road Safety Corps) ta Jihar Bauchi, Mista Rilwan Suleiman, ya bada tabbacin ga manema labarai a wata sanarwa ta kan wayan Salula.

A bayanin Rilwan “Lallai da gaske ne abin ya faru. Wata Motar Hilux da ke  dauke da lamban Gwamnati ta ci karo da Motar Tanki da ke dauke da Man Fetur, a nan take kuma mutane biyu suka mutu. wasu kuma sun samu mugun raunuka”

“A halin yanzu ina tabbatar maku da cewa Hukumar mu na kan bincike da kuma kula da lamarin.” inji bayanin shi da manema labarai a lokacin da abin ya faru.

Idan akwai wata bayani da ya biyo baya game da wannan, zamu sanar da shi a shafin Hausa.NaijaNews.com