Connect with us

Uncategorized

Gwamna Ganduje, Gawuna da ‘Yan Majalisa 27 a Kano sun karbi takardan komawa ga Mulki

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Laraba, 3 ga watan Afrilu 2019, Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben Kasa, INEC ta Jihar Kano ta baiwa Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna da sabbin ‘yan gidan Majalisu 27 sun karbi takardan komawa ga kujerar shugabanci.

Ko da shike, Naija News ta gane da cewa ‘yan gidan Majalisar wakilan Jihar daga Jam’iyyar adawa, PDP sun kaurace wa hidimar karban takardan komawa ga kan shugabancin Jihar da aka yi a gidan Wasannai ta Sani Abacha da ke a Jihar.

“Ku dauki hali iri ta gari. Ku kuma gane da cewa hidimar siyasa ba hidimar dole-ko-ta-yaya bace” inji Engr. Abubakar Nahuche, babban Malamin zabe da ya Jagorancin Hidimar zaben Jihar, Kano, Katsina da kuma Jihar Jigawa. Ya fadi hakan ne a yayin da yake mikar da takardu ga ‘yan siyasan.

Ya kumar taya su murna da kara shawartan su da cewa kada su manta da mutanen da suka zabe su ga kujerar shugabanci.

“Ku tuna da mutanen da suka kai ku ga kujerar shugabanci” inji shi.

Karanta wannan kuma: APC tayi sabuwar rashi a yayin da Alhaji Faruk da Matarsa sun kone da wuta har ga mutuwa a Jihar Kebbi.