Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 3 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 3 ga Watan Afrilu, 2019

1. Majalisar Dattijai sun gabatar da yadda za su tafiyar da kasafin kudi ta 2019

Gidan Majalisar Dattijai sun bayyana da cewa zasu gabatar da kasafin kudin kasa ta shekarar 2019 a ranar 16 ga watan Afrilu.

Naija News ta gane da hakan ne a yayin da shugaban gidan Majalisar, Sanata Bukola Saraki ya gabatar da hakan a ranar Talata da ta gabata da bada umarni ga kwamiti na kasafin kudin da su bayar da rahoton su daga ranar 9 zuwa 11 ga watan Afrilu.

2. Kotu ta gabatar da cewa Adeleke bai dace da takaran kujerar Gwamna ba

Kotun Koli ta birnin Abuja a ranar Talata da ta gabata, ta gabatar da dakatar da Sanata Adeleke, dan takaran kujerar Gwamnan Jihar Osun daga Jam’iyyar PDP da zama Gwamnan Jihar.

Kotun tayi hakan ne bisa wata Kara da zargin da wasu jigo biyu daga Jam’iyyar APC suka yi ga Adeleke da cewa bai da cikakken takardu na takaran kujerar Gwamna.

3. Wike ke kan nasara ga hidimar zaben Jihar Rivers

A yayin da ake gabatar da sakamakon zaben kananan hukumomin Jihar Rivers ga zaben kujerar Gwamnan Jihar, sakamakon ya bayyana da cewa Nyesom Wike, dan takara daga Jam’iyyar PDP ne ke kan bisa yawar kuri’u.

Dan takaran Jam’iyyar PDP ya lashe zaben karamar hukumar Ikwerre da yawar kuri’u 14, 938 bisa Rotimi Amaechi, Ministan Sufuri, da ya samu yawar kuri’u 5, 660 daga jam’iyar AAC.

4. Hukumar JAMB ta gabatar da sabon ranar da za a fitar da takardan shiga jarabawar shekarar 2019

Haddadiyar Hukumar Tafiyar da Jarabawan shiga Makarantan Jami’a Babba (JAMB), ta gabatar da sabon ranar da za a fitar da takardan shiga jarabawan JAMB ta shekarar 2019/2020.

Mai yada labarai ga Hukumar, Dakta Fabian Benjamin ya gabatar da hakan ne ranar Talata da ta gabata ga manema labarai a birnin Abuja da cewa Hukumar ta daga ranar fitar da takardan shiga jarabawan zuwa ranar 4 ga watan Afrilu 2019. Watau ranar Alhamis ta makon nan.

5. Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya (NAF) tayi sabon nasara da ‘yan Ta’addan a Jihar Borno

Rundunar Sojojin Sama ta kasar Najeriya (NAF) da aka fi sani da ‘Operation LAFIYA DOLE’ ta bayyanar da sabuwar nasara da suka yi kan kungiyar ‘yan ta’addan Islam (ISWAP) ta Jihar Borno.

Naija News Hausa ta gane da cewa Rundunar sun yi nasara ne da rukunin ‘yan ta’addan da ke a yankin Magari a shiyar Chadi ta Jihar Borno.

6. Kotu tayi watsi ga wata Karar da wasu ke yi don dakatar da hidimar zaben Jihar Rivers

Kotun Koli ta Abuja, tayi watsi ne da karar da Jam’iyyar (AAC) suka gabatar game da zaben Gwamnan Jihar da aka yi a baya ranar 9 ga watan Maris 2019.

Naija News Hausa ta gane da cewa Jam’iyyar AAC sun yi karar Hukumar INEC ne akan ci gaba da hidimar zaben Jihar.

7. Hukumar INEC ta bayyana lokacin da zata dauki mataki ga zaben Firamare na Jihar

Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben Kasar Najeriya, INEC sun bayyana da cewa zasu jira har sai Kotun Kara ta bada umarni bisa karar da ake yi kamin dada hukumar su ta dauki nasu mataki, akan zaben firamaren Jihar Zamfara.

Muna da sani a Naija News da cewa Hukumar INEC ta ki bayar da takardan komawa ga kan mulki ga Mukhtar Shehu, Gwamnan Jihar, bisa umarni da shari’ar da Kotun Koli ta Jihar Sokoto ta bayar.

8. Ka tsari kanka – Jam’iyyar APC sun gayawa Sanata Saraki

Jam’iyyar Shugabancin Kasa, APC sun kalubalanci shugaban Sanatocin kasar Najeriya, Sanata Bukola Saraki da Jam’iyyar Adawa, PDP da cewa su tsari kansu, su kuma janye bakin su daga zaben sabon shugaban Gidan Majalisar Dattijai.

“Ba ruwan Jam’iyyar Adawa da yadda zamu tafiyar da shugabancin mu. Bai dace ga bakin su da bamu shawara ba” inji APC.

9. PDP ta lashe dukan zaben Kujerar Sanata na Jihar Rivers

Bisa zaben da aka yi a Jihar Rivers, Jam’iyyar Dimokradiyya, PDP ta lashe dukan kujerar tseren Sanata na Jihar.

‘Yan takaran Ukku; George Sekibo daga gabashin Jihar Rivers, Bari Mpigi daga Kudu maso Gabas ta Rivers da kuma Betty Apiafi daga Yammacin Jihar Rivers, suka lashe zaben su da yawar kuri’u bisa ‘yan adawan su.

 

Ka samu cikkakun labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com