Connect with us

Uncategorized

Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna sun kashe barayi ukku a Jihar a wata ganawar wuta.

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Bisa bincike, Naija News Hausa ta gane da cewa ‘yan sandan sun yi ganawar wutan ne a yayin da wasu barayi biyar suka fada wa wata kamfani da ake ce da ita ‘MotherCat’ a shiyar Mando ta Kaduna.

Abin ya faru ne missalin safiyar ranar Laraba da ta gabata inda barayin suka fada wa ‘yan sandan da ke tsaron kamfanin da munsayar harsasun bindiga.

Da ganin hakan, ‘yan sandan sun mayar da wuta ga barayin, sun kuma ci nasara da kashe ukku daga cikin barayin. Ko da shike biyu sun yi gudun hijira daga munsayar wutan ‘yan sandan.

An bayar da cewa biyu daga cikin ‘yan sandan sun samu raunuka da yawan gaske, an kuma kai su a asibitin Rudunar Sojoji da ke a Jihar Kaduna don bayar da kulawa ta gaske.

Don karin tabbaci game da ganawar wutan, Kakakin yada yawu na ‘yan sandan Jihar, Yakubu Sabo, ya bayyana da cewa barayin sun fada wa ‘yan sandan ne bayan da suka samu shiga kofar kamfanin.

Ya kara da cewa barayin sun fada wa kamfanin ne a missalin karfe biyar na safiyar ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu 2019 da ya gabata, “A yayin da suka samu shiga kofar kamfanin, wuf sai suka fada wa darukan tsaron da ke a wajen da hari”

“A ganawar wutan, jami’an tsaron mu biyu, Insfekta Bijimi Maiyaki, da SGT. Kabiru Shuaibu sun yi mumunar raunuka daga harin, amma dai suna samun kulawa ta gaske a asibi” inji Yakubu.

“Ko da shike, NCO ya mutu a yayin da ake masa kulawa, amma dai shi Insfektan na da rai, kuma an sallame shi daga asibiti”

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Gwamnatin Jihar Zamfara ta kafa dokar Zama daki Rufe ga dukan Kananan hukumomin Jihar bisa Matsalar tsaro