Uncategorized
Jihar Gombe ta rasa Kayaki mai kimanin Miliyan N388m a wata sabuwar Gobarar Wuta
A yau Alhamis, 4 ga watan Afrilu 2019, Hukumar Kashe Yaduwar Gobarar Wuta ta Jihar Gombe sun gabatar da ribato rayukan mutane kusan 426 a wata gobarar wuta da ya kone kayaki mai tsadar naira miliyan N388.
Hukumar ta gabatar ne da sanarwan ne daga bakin wani Ofisan Hukumar Yaki da Kashe Gobarar Wutan Jihar, Malam Salihu Mahmoud a wata ganawa da yayi da manema labarai a yau a nan garin Gombe.
Malam Salihu ya bayyana ga manema labarai da cewa hukumar su ta karbi irin wannan kirar gaugawa ta gobaran wuta a Jihar kusan sau 107 tsakanin wannan shekarar.
Ko da shike ya bayyana da cewa ba wanda ya mutu sakamakon gobarar. ya kuma kara da cewa hukumar na iya kokarin su da ganin cewa sun magance matsalar gobarar wuta a Jihar, musanman, tabbatar da cewa ba a samun rashin rayuwa idan ma hakan ya faru.
Malam Salihu ya gabatar da cewa wannan nasarar da hukumar ke samu sanadiyar biyayya ne na mutanen Jihar bisa Ilimantarwa da aka masu akan yaki da gobaran wuta, kuma mutane na bin hakan. inji shi.
Ya karshe da kara karfafa al’ummar Jihar da tabbatar da cewa suna gyara duk wata likin wutar lantarki da zai iya jawo gobara.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Kimanin gidaje 60 suka kone kurmus a wata gobarar wuta a Jihar Jigawa. Dabbobi da kayakin rayuwa ta al’umma duk ta kame wutar. Abin ya faru ne a kauyan Barebari da ke a karamar hukumar Ringim ta Jihar Jigawa kwanakin baya.