Connect with us

Uncategorized

Kalli wani Magidanci da ke sana’ar sayar da Fanke

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta gano hoton wani mutumi da ke sana’ar sayar da fanke a Kuducin kasar Najeriya.

Rayuwa kan zama da matsala sosai wasu lokatai, ci da sha abin mamaki ne ga rayuwar wasu a koyaushe. Wannan mutumin ya dauki kadar rayuwa, bai raunana ga karfi da irin hikimar da Allah ya bashi ba, ya gane da cewa da yayi sata ko fada kan hanya da roko, gara ya yi wannan sana’a don taimaka wa rayuwar sa.

Bisa ganewar wannan gidan labarai tamu, an gabatar da cewa mutumin na da Iyali, dan Makarantan Babban jami’a ne kuma na UNIUYO.

A halin yanzu hoton mutumin ya mamaye ko ta ina a layin yanar gizo, musanman Twitter. Mutane da dama sun yaba masa da irin wannan mataki da kuma kuzari.

Mutane da masa addu’a da fatar alkhairi ga rayuwa, musanman Allah ya sa ya dace wata rana da mai taimaka masa da abin rayuwa isasshe.

An bayyana da cewa da wannan sana’ar ne mutumin ke ciyar da kansa, Iyalin sa da kuma biyar kudin makaranta.

Kalli hoton mutumin a layin Twitter, kamar yadda wani ya rabas;

Kalli bayanin wasu game da rayuwar mutumin;