Connect with us

Uncategorized

Kannywood: Kalli Jerin Masu Arziki Goma, na sama a Kannywood

 

Kannywood itace likin suna da aka baiwa hadaddiyar ‘yan shirin fim na kabilar Hausa, musanman Arewacin kasar Najeriya. Suna kuma da Hedkwatan su a Jihar Kano. Naija News Hausa na da sanin cewa Kannywood na daya daga  manyan kanfanin shirin fim a Afrika da kuma kasar Najeriya.

An samu sunan “Kannywood” ne a shekararun baya, bisa 1990s kamar yadda tarihi ta bayar. Sunan kuma ta tsiro ne daga bakin Sunusi Shehu, jigo daga ‘Tauraruwa Magazine’. Sunan ta samu shiga fagen nishadi da kyau ne a shekarar 1999.

Atun wannan lokacin kuwa, ‘yan shiri da dama sun yi taken fasaha da kuma tsalon iya shiri na kowace iri. A yau, Allah ya jikan rai, wasu daga cikin manyan wannan kanfani sun zama abin labari, a yayin da wasu sun mutu, wasu kuma sun tsufa.

Masu Kudi a Kannywood:

A kassa, Naija News Hausa zata gabatar da masu arziki goma na sama a shafin Kannywood.

Kalla;

1. Ali Nuhu

Shahararran jigo da dan shirin wasan Kannywood, Ali Nuhu, ya fito na daya bisa bincike a layin masu arziki a shafin Kannywood.

Bincike ya bayyana da cewa Ali Nuhu na da Manyan Gidaje da kuma wata babbar Hotal a Jihar Bauchi. Ali Nuhu kuma Ambasada ne a manyan kanfanoni a kasar Najeriya, kamar su  GlO, OMO, SAMSUNG dadai sauran su.

Ali na kuma daya ne daga cikin tsohon ‘yan shirin fim na Kannywood tun lokacin da aka kafa kanfanin. Ba a Kannywood kawai ba, Ali Nuhu na fita shirin fim har ga Nollywood da Bollywood. Ya kuma samu fita fina-finai da dama.

Karanta wannan kuma: Kalli yadda masoya suka taya Ali Nuhu murna da ranar Haifuwa

2. Adam A. Zango

Adam A. Zango ya fito na biyu cikin wannan tsarin. Ba zaka yi hirar kannywood ba, ba tare da ka ambaci Adam ba. Shahararre ne da kuma jigo a wannan kanfanin.

Adam na daya daga cikin ambassada na kanfanin sadarwa na MTN. Wannan ya nuna irin kudin da Adam ke karba a kowace wata. Yana kuma da wata babbar gidan zama a garin Kaduna. Adam mawaki ne kuma na kwaran gaske. Ko da shike a baya yayi barazanar barin kanfanin kannywood. Amma bincike da ganewa ya bayyana da cewa Adam ya koma ga shirin fim.

3. Dauda Kahutu Rarara

Ga wani dan siyasa anan, Dauda Kahutu Rarara. Na Ukku ga masu kudi a Kannywood. Rarara sosai a kannywood, musanman a hidimar siyasa kuma. Idan zaka yi hirar mawaka a kannywood ko Arewacin kasar Najeriya, dole ne ka ambaci ‘Rarara’ kamar yadda aka fi sanin sa da suna.

Mun tuna a Naija News Hausa da cewa Rarara na daya daga cikin mawakan da suka raira waka wajen hidimar neman zaben shugaba Muhammadu Buhari a hidimar zaben 2019 da aka kamala a watan Maris.

4. Nura M. Inuwa

Inuwa ya fito na Hudu a wannan layin. Shima mawaki ne na kwaran gaske a kannywood. Mai arzikin gaske ne kuma daga cikin ‘yan shirin fim na Arewacin kasar.

5. Halima Atete

Tau, abin bai tsaya ga Maza kawai ba, Halima ita ma shaharrarar ‘yar shirin fim ne a Kannywiod. Mai arziki ce kuma daya daga cikin kyakyawan mata a kamfanin kannywood.

6. Sani Danja

Hirar Kannywood ba tare da sunan Sani danja ba, lallai wannan hirar ba ta cika hira ba. Danja na daya daga cikin Manyan ‘yan shirin fim da suka dade a Kannywood. Yana da arzikin na kwaran gaske, shima yana da wata babbar gida birnin Abuja.

Karanta takaitaccen labarin Sani Danja, kamar yadda muka sanar a Hausa.NaijaNews.Com

7. Sadik Sani Sadik

Idan kana neman masu son nishadi da adon jiki, tau ka nemo Sadik Sani Sadik. Shaharare ne a Kannywood, Matashin Mai Arziki ne Sadik. Sadik shima na da Awad da daman da ya karba a fagen shiri, saboda irin nasa salon shirin.

8. Nafisa Abdullahi

Idan kana hirar kyakyawan ‘yan Mata a Kannywood, tau lallai sai fa ka hada da ambatan Nafisa Abdullahi. Ita ma shaharrara ce a fagen shirin fim na Kannywood. Tana da irin na ta Arziki kuma fiye da ‘yan uwan ta.

Nafisa na da masoya na yawan gaske a shafin nishadarwa.

9. Hadiza Gabon

Hadiza Gabon wata fitaciya ce a kamfanin Kannywood. Ita ma Kyakyawar Macce ce da fasaha wajen shirin fim. Arzikin ta ba abin ja da baya bane.

10. Aisha Aliyu Tsamiya

Na karshe a wannan lissafi tamu itace Aisha Aliyu Tsamiya. Mace mai kyan kallo da armashin salo. Shaharara ce kuma mai arziki a Kannywood.

Continue Reading
Advertisement
Advertisement
close button