Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 4 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 4 ga Watan Afrilu, 2019

1. Shugaba Buhari ya gabatar da bacin rai game da kisan Kolade Johnson da aka yi

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana bacin rai da kuma isar da gaisuwa jinya ga Iyalin Kolade Johnson, wani da ‘yan sanda suka harbe har ga mutuwa a Jihar Legas.

Naija News ta ruwaito a wata sanar da cewa Hukumar SARS ta ‘yan sandan Najeriya sun kashe Kolade a wata gidan kallon wasan kwallon kafa. Hakan ya faru ne a yayin da ‘yan sandan ke zaton cewa Kolade dan ta’adda ne ganin irin shirin da yayi zuwa, musanman suman kan sa.

2. APC ta kalubalanci Saraki da Dogara game da shugabancin Gidan Majlisa ta 9

Mataimaki ga Sakataren Yada labarai ga Jam’iyyar APC ta tarayya, Yekini Nabena ya kalubalanci shugaban gidan Majalisar Dattijai, Sanata Bukola Saraki da Kakakin gidan Majalisar, Yakubu Dogara da cewa su janye  hannun su daga hidimar shugabancin Gidan Majalisar.

Yekini ya fadii hakan ne a wata ganawa da manema labarai a ranar Laraba da ta gabata a birnin Abuja.

3. Gwamnatin Jihar Zamfara ta kafa Dokar Kulle ga jama’ar Jihar

Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya gabatar da zaman daki kulle da Jihar a ranar Laraba da ta gabata.

Naija News Hausa ta sanar da baya da cewa Yari ya bayar da umarnin zaman daki kulle ga Jihar Zamfara na tsawon awowin karfe bakwai na dare zuwa karfe bakwai na safiya.

4. INEC ta bayar da takardan komawa kan mulki ga Ganduje

Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da Mataimakin sa Nasiru Yusuf Gawuna hade da wasu ‘yan Majalisar Wakilan Jihar 27 sun karbi takardan komawa ga kujerar shugabancin Jihar daga hannun hukumar INEC.

Ko da shike an bayyana da cewa ‘yan Majalisa 13 daga Jam’iyyar PDP sun kaurace wa hidimar karban takardan shugabancin.

5. Shugaba Muhammadu Buhari ya zargi Gidan Majalisa da kara ga bashin Jihohi

Wannan itace karo ta biyu da Shugaba Muhammadu Buhari ke zargin Gidan Majalisar Dattijai da kara ga kasafin bashin da Gwamnatin Tarayya zata biya ga Jihohin kasar.

Naija News ta gane da hakan ne a yayin da shugaban ya bukaci ‘yan Majalisa da mikar da kasafin kudin da za a bayar ga Jihar Delta da Taraba.

6. Kungiyar Iyamira, IPOB sun yi watsi da zargin kone Ofishin ‘yan Sanda

A ranar Laraba da ta gabata, Kungiyar ‘Yan Biafra (IPOB), sun bayyana rashin amincewa da zargin da ake yi da su na Kone wata Ofishin ‘yan Sandan Jihar Anambra.

A wata sanarwa ta ranar Litini, Naija News ta sanar da cewa an ‘yan sanda sun kame wasu mutane biyar da ake zargin su da kone Ofishin Jami’an tsaro da ke a yankin Ajali, ta karamar hukumar Orumba.

7. Nwosu ya gabatar da kara game da zaben Jihar Imo

Uche Nwosu, dan takaran tseren Gwamnan Jihar Imo daga Jam’iyyar (AA), kuma Surukin tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, ya gabatar da karar rashin amincewa da sakamakon zaben Jihar.

Nwosu, ya bayyana a ranar Talata da ta wuce da cewa Jam’iyyar APC ne sanadiyar da ya sa ya fadi ga tseren takaran kujerar Gwamnan Jihar.

8. Kungiyar Tallafi ta (IMF) sun shawarci shugaba Buhari da janye tallafin Man Fetur

Hukumar Bada Tallafi ga Kasar Tarayya (IMF) ta shawarci Gwamnatin Tarayya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari da janye tallafin Man Fetur, da kuma wade biyar haraji don taimaka wa bankuna da suka raunana.

Hukumar ta gabatar ne da hakan ga shugaba Buhari don karfafa yaduwar tattalin arzikin kasar.

Ka sami cikakken labaran kasar Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com