Connect with us

Uncategorized

Wani Mahaukaci ya Kashe Dan Sanda a Jihar Kwara

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Jami’an Tsaro ta Jihar Kwara sun gabatar da cewa wani mutumi da ake dubin shi da tabuwar kwakwalwa, ya kashe daya daga cikin ofisan tsaron su da tsaran Adda.

Bisa bayanin da hukumar ta bayar, Naija News Hausa ta gane ne da cewa mahaukacin ya hari Sgt. Abu ne da Adda a ranar Talata da ta gabata a yayin da yake kan tsaro cikin kewayan Ofishin su da ke a yankin Omu-Aran, Arewacin Jihar Kwara.

An bayyana da cewa an haura da kai Mista Abu a wata Asibitin kamin dada aka kara gaba da shi a Babban Asibitin da ake kira ‘Ido Medical Centre’ a Jihar Ekiti, a inda ya mutu a ranar Laraba da ta gabata.

A bayanin wani da ya samu ganin al’amarin, ya gayawa manema labarai a haka,  “Ina saman Babur di na ne da na ga mutumin mai Alamun tabuwar kwakwalwa yadda ya ke saran dan sandan da Adda da kuma bungun Icce”

“Na bi shi da gudu hade da wasu ‘yan kabukabu. Ya kama hanyar Taiwo da gudu muna biye da shi, ‘yan lokatai kadan sai ya tsaya, ya kuma mika hannun sa biyu a sama, da alamun saranda” inji shi

“Anan take ‘yan sanda suka biyo da kame shi, suka kuma tafi dashi a Ofishin su”

Mista Ajayi Okasanmi, Kakakin yada yawun jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar, ya bayyana da cewa hukumar su na kan bincike akan lamarin.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Hedkwatan Rundunar Sojojin Najeriya ta ‘Operation Whirl Stroke’ (OPWS) sun ci karo da wasu mutane biyu da ake zargin su da kirar bindigogi. sun gane da hakan ne a wata zagayen bincike da suka yi a Jihar Nasarawa, Taraba da Jihar Benue.