Uncategorized
An Kame ‘Yan Hari da suka sace Sheikh Ahmad kwanakin baya

Hukumar tsaro sun ci nasara da kame ‘yan ta’adda da suka sace Sheikh Ahmad Sulaiman kwanakin baya kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa da cewa wasu ‘yan hari da bindiga sun sace Sheikh Ahmad a kan hanyar Jihar Kebbi.
An gabatar da kame Lawal Ibrahim ne da mambobin kungiyar ta’addancin a yayin da suke kokarin shiga yankin Jihar Kogi.
Shugaban kungiyar ‘yan harin, Ibrahim, ya bayyana a wata bidiyo da cewa wasu mambobin kungiyar sun kashe junansu bayan da suka saki Sheikh Ahmad a baya. Naija News ta ruwaito a baya da cewa ‘yan harin da suka sace Sheikh Ahmad sun sake shi bayan ‘yan kwanaki.
Bisa bayanin Ibrahim da wani mamban kungiyar harin mai suna Isiyah, sun bayar ga manema labarai da cewa lallai su goma ne suka kadamar da sace Sheikh Ahmad, watau Babban Malamin Arabi da mai bada addu’a ga shugaba Muhammadu Buhari ga hidimar neman zaben shugabancin kasa a zaben da aka kamala.
Ya bayyana da cewa bai taba ganawa da Alhaji Dogo Nalade ba, “Akan wayar salula ne kawai muke hira a kowane lokaci da Alhaji Dogo, bamu taba ganawa ido-da-ido ba”
Ibrahim ya bayyana da cewa lallai Alhaji Dogo ne ya umarce su da kadamar da sace Sheikh Ahmad.
“An kame mu ne a yayin da muke kokarin gujewa daga kangin mu zuwa shiyar Obajana, a jihar Kogi don neman aikin yi bayan da muka amince da barin aikin sace-sacen mutane” inji shi.
“Mu kan karbi makamai ne daga hannun wa ‘yanda ke bayar da aikin sace mutane a gare mu. Idan kuma mun kamala aikin mu, sai a biya mu kudin mu”
“Yadda muka saki Sheikh ya zama abin mamaki a garemu. duk da bukatar mu da iyalan sa da biyar kudi kamin mu sake shi, hakan bai faru ba, kuma a baya muka sake shi ba tare da karban ko taro ba”
“Farmaki ya tashi ne tsakanin ‘yan kungiyar tamu, daga nan sai muka dingi harbin juna da bindiga. Da na gane da hakan, sai ni da Isiya muka fada daji da gudun hijira, sauran kuma sun kashe junansu”
Ya karshe da cewa a yayin neman tsiran ne suka fada ga hannun hukumomin tsaro da suka kame su.