Uncategorized
Gobarar wuta ya kame Shaguna Takwas a Jihar Katsina
A yau Jumma’a, 5 ga watan Afrilu, Hukumar Yaki da Gobarar Wuta ta Jihar Kano sun gabatar da cewa gobarar wuta ya kone shaguna takwas a safiyar ranar Jumma’a ta yau a shiyar Randabawul ta Muletara da ke Karamar Hukumar Ungogo ta Jihar.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Gobarar wuta ya kame wani Makarantar Sakandiri a Jihar Kano
Alhaji Saidu Mohammed, Kakakin Hukumar ya bada tabbacin hakan ga manema labarai da cewa abin ya faru ne a missalin karfe shidda na safiyar yau (Jumma’a).
Ya gabatar da cewa sun karbi wata kirar gaugawa a Ofishin su daga bakin wani da ke a shiyar da abin ya faru.
“Hukumar mu da ke yankin Dawanua ta karbi Kirar gaugawa ne da safiyar yau Jumma’a daga bakin Aliyu Mansir da cewa gobara ya kame wasu shaguna a shiyar Randabawul ta Muletara” inji Mista Saidu.
“Da jin hakan, Hukumar mu ta yi wuf da motar kashe wuta tare da Ma’aikata zuwa wajen da abin ya faru. motar ta isa wajen ne da Ma’aikata missalin karfe bakwai da sauran ‘yan mintoci (6:58am). Ma’aikata kuma suka dakatar da yaduwar wutar” inji shi.
Ko da shike, a wannan lokacin, ba a iya bayyana ko menene ya jawo sanadiyar gobarar wutan ba, amma dai an samu kashe wutar daga yaduwa.