Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 5 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 5 ga Watan Afrilu, 2019
1. Shugabancin kasa ta gabatar da alkawalai da shugaba Buhari yayi da kuma yadda ya cika su
A ranar Alhamis 4 ga watan Afrilu da ta gabata, shugabancin kasar Najeriya ta gabatar da cewa lallai shugaba Muhammadu Buhari ya cika alkawalan shi ga ‘yan Najeriya duka.
Mista Femi Adesina, Mai bada shawara ga shugaba Muhammadu Buhari ne ya gabatar da hakan a wata sanarwa da aka bayar ga Naija News.
2. Kotun Koli ta bukaci Saraki, Melaye da Murray-Bruce da bayyanar da kansu ga ‘yan sanda
Kotun Koli ta Abuja, babban birnin Abuja, ta kalubalanci shugaban gidan Majalisar Dattijai, Sanata Bukola Saraki, da Sanata Dino Melaye da kuma Sanata Ben Murray-Bruce da bayyana kansu ga Jami’an tsaro bisa wata karar da ake da su tun ranar 5 ga watan Aktoba ta shekarar 2018 da ya gabata.
Ka tuna da cewa Jam’iyyar APC sun umarci Saraki da Jam’iyyar PDP da janye bakin su daga yadda za a tafiyar da zaben sabon shugaban ‘yan majalisa.
3. Kotun Kara ta Jihar Kano ta shawarci ‘yan siyasa da janye hannu ga hidimar karar da ake akai
Kotun Kara ta Jihar Kano da ke jagorancin karar hidimar zaben Gwamnoni, Gidan Majalisar Dattijai da Wakilai ta kalubalanci ‘yan siyasa da janye bakin su da shiga zance karar da kotun keyi game da zaben Jihar.
Kotun ta gabatar ne da hakan daga bakin Alkali Nayai Aganaba, Ciyaman na rukunin Karar, a ranar Alhamis da ta gabata a Jihar Kano.
4. Ba a gabatar da gaskiya ga shugaba Buhari ba game da zancen bashin Jihohi – Saraki
Shugaban Sanatocin Nejeriya, Sanata Bukola Saraki ya bayyana da cewa watakila shugaba Muhammadu Buhari bai samu cikakken bayani ba game da zancen bashin da Jihohi ke bin Gwamnatin Tarayya.
Sanata Saraki ya dage da cewa Gidan Majalisa ba ta kara ba bisa kasafin kudin da Gwamnatin Tarayya zata biya ga Jihohi.
5. Jam’iyyar APC sun yi bayani game da shugabancin gidan majalisar dattijai
Jam’iyyar da ke shugabancin kasar Najeriya, APC sun bayar da dama ga Sanata Ali Ndume daga kujerar sanata a Jihar Borno ga fita tseren takaran kujerar shugabancin gidan Majalisar Dattijai da fuskantan Sanata Ahmed Lawan.
Jam’iyyar ta gabatar ne da hakan ga manema labarai a wata ganawa da kakakin yada labarai ga jam’iyyar, Malam Lanre Issa-Onilu.
6. Kotun Koli ta Abuja ta janye zancen sayar da kamfanin Etisalat
Kotun Koli ta bayyana janye zancen sayar da kamfanin sadarwa ta Najeriya, Etisalat da aka canza wa suna zuwa 9mobile ga kamfanin Teleology.
Kotun ta bayyana hakan ne daga bakin Alkali Binta Nyako, da ke jagoracin karar.
7. Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi kasar Jordan da Dubai
Naija News Hausa ta sanar a baya da cewa shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci kasar Jordan da Dubai don halartan wata zaman tattaunawa game da tattalin arzikin kasa.
Shugaba Buhari ya bar kasar Najeriya ne zuwa kasar Jordan ranar Alhamis da ta gabata don ya halarci gayyatan King Abdullah II bin Al-Hussein na kasar Jordan.
8. Dalilin da yasa shugaba Muhammadu Buhari yaki sanya hannu ga kankanin albashin ma’aikata
Shugabancin kasa ta bayyana dalilin da ya sa shugaba Muhammadu Buhari bai harwayau rattaba hannu ga takardan kankanin albashin ma’aikata ba.
Naija News Hausa ta sanar a baya da cewa Gidan Majalisa ta gabatar da takardan dokar biyan kankanin albashi na naira dubu N30,000 ga ma’aikatan kasa tun ranar 19 ga watan Maris da ya gabata.
Ka samu karin bayanai ga labarun Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com