Connect with us

Uncategorized

Fankan Jirgin Sama ya Guntse Kan wani Matukin Jirgin Rundunar Sojojin Najeriya

Published

on

at

A karshe makon da ta gabata, rundunar Sojojin sama ta Najeriya sun gabatar da rasa daya daga cikin masu tuka jirgin saman rundunar.

An bayyana da cewa Mista Umar, Matukin Jirgin Saman Rundunar ya mutu a wata zagayen yaki da rundunar suka kai wa ‘yan ta’adda a yankin Bama ta Jihar Borno.

Daya daga cikin Sojojin da ya samun cikakken sani da ganin yadda abin ya faru, ya bayar ga manema labarai da cewa abin ya faru ne a nan yankin Bama da maraicen ranar Asabar da ta gabata. Bisa bayanin shi, jirgin saman ta samu matsala ne hakan ya faru.

“Marigayin ya je ne garin daukan jakkan sa daga saman jirgin, a yayin saukowa ne ya daga kansa a sama, wuf sai fanka jirgin ya guntse masa kai” inji shi.

Ya kara da cewa al’amarin ya faru ne missalin karfe hudu na maraicen ranar Asabar da ta gabata.

“An riga an sanar ga Iyalan Umar game da abin da ya faru. Ana kuma kan shiri game da hidimar zana’izar sa” inji Sojan a lokacin da ya gana da manema labarai.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Rundunar Sojojin Najeriya sun yi sabuwar rashi a yayin da ‘yan hari da makami suka kashe daya daga cikin kwamandan sojojin kasar a Jihar Bauchi.

‘Yan hari da bindiga a ranar 18 ga watan Maris, 2019 sun kashe Col. Mohammed Barack, Kwamandan rukunin ‘Garrison Commander, 33 Artillery Brigade of Nigerian Army da ke barikin Shadawanka, a nan Jihar Bauchi.