Connect with us

Uncategorized

Gwamna Dankwambo ya Rantse da cewa ba zai janye daga Jam’iyyar PDP ba

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo yayi rantsuwa da cewa ba zai yi murabus da Jam’iyyar dimokradiyya, PDP ba.

“Lallai an ci amanar Jam’iyyar PDP a zaben kasa da aka gudanar ‘yan makonnai da suka gabata a Jihar Gombe, amma lokaci ba ta karya.” inji Dankwambo.

Dankwambo kara gabatar da cewa da shi, da sauran masoyan jam’iyyar dimokradiyya, PDP da suka ki janyewa daga Jam’iyyar PDP ba tun hidimar zaben jam’iyyar 2015, ba za su yi hakan ba a yanzu.

“Mutane da dama sun ci amanar Jam’iyyar mu a zaben baya ta Jihar Gombe, amma dai lokaci zai wanke mu daga duk wata tuhuma. Ko da shike matakin da suka dauka ya zafe mu da  gaske, amma lokaci zai bayyana” inji shi.

“A matsayi na na mamban Jam’iyya mai biyayya, ban janye daga Jam’iyyar ba a hidimar zabe ta shekarar 2015 da ya wuce, kuma ba zan taba yin hakan ba” inji shi.

Naija News Hausa a baya ta ruwaito da cewa Gwamna Ganduje, Gawuna da ‘Yan Majalisa 27 a Jihar Kano sun karbi takardan komawa ga Mulki