Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litinin, 8 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

 

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litinin, 8 ga Watan Afrilu, 2019

1. Gwamnatin Tarayya ta dakatar da haƙa ma’addinai a Jihar Zamfara

Gwamnatin Tarayya ta kasar Najeriya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, ta bada umarni ga Kamfanonin haƙa ma’addinai ta Jihar Zamfara da dakatar da ayukan su da kuma tayar da kamfanonin su daga Jihar.

Shugaban Jami’an tsaron ‘yan Sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu ne ya gabatar da hakan a wata gabatarwa da yayi ga gidan Majalisar Jihar a ranar Lahadi da ta gabata a birnin Abuja.

2. Hukumar INEC da Jam’iyyar APC zata mayar da Martani ga Atiku kamin ranar Alhamis ta gaba

Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben Kasar Najeriya, INEC na da tsakanin nan da zuwa ranar Alhamis ta gaba don mayar da martani ga Jam’iyyar PDP da dan takaran kujerar shugaban kasa daga Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, game da karar rashin amince da sakamakon hidimar zaben shugaban kasa da Atiku yayi a kotun kara.

An kuma baiwa Shugaba Muhammadu Buhari daga nan har ranar 16 ga watan Afrilu don mayar da martani game da zancen.

3. Ba a taba Gwamna mara amfani ba a Najeriya irin Gwamnan Zamfara – inji Kadaria

Shaharariyyar mai watsa labarai da kumar wallafa labarai, Kadaria Ahmed, ta fada da cewa kasar Najeriya ba ta taba samun Gwamnan Jiha mara amfani ba a tarihi, kamar irin Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari.

Naija News ta gane da wannan rahoton ne a wata gabatarwa da Kadaria ta yi da sauran manema labarai a birnin Abuja a wata ganawan  tattaunawa game da kashe-kashe da ake yi a Jihar Zamfara.

4. Wata Sabuwar Kunar Bakin Wake ta kashe kimanin mutane biyar da barin wasu da raunuka a Borno

Kimanin mutane biyar suka rasa rayukan su a wata sabuwar harin ‘yan kunan bakin wake da aka yi a Maiduguri ta Jihar Borno.

Harin ta bar mutane kusan arba’in da biyar (45) da raunuka a yayin da ‘yan ta’addan suka hari wata shiyya da ake cewa Muna-Dalti a garin Maiduguri, a daren ranar Asabar da ta wuce.

5. PDP na zargin Jam’iyyar APC da kulla tayar da hankali a Jihar Rivers

Jam’iyyar PDP na zargin Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da Ministan Kara ta Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami da hada kai da Kotun kara don kadamar da tashin hankali a Jihar Rivers.

Kakakin yada yawun Jam’iyyar PDP, Mista Kola Ologbodiyan na zargin babban Alkalin kasar Najeriya, CJN Tanko Mohammed da cewa alkalin na cikin halin tsanani daga manyan Jam’iyyar APC don janye shari’ar da Kotu ta yi a baya na dakatar da ‘yan Jam’iyyar APC daga hidimar zaben Jihar Rivers.

6. Ndume yayi watsi da zancen janyewa daga tseren shugabancin Gidan Majalisar Dattijai

Sanata Ali Ndume ya nuna rashin amincewa da bukatar Jam’iyyar APC da shugaban Jam’iyyar APC ta Tarayya, Asiwaju Bola Tinubu, na cewar ya janye daga takaran shugabancin gidan Majalisar.

Naija News Hausa ta gane da cewa shugabancin Jam’iyyar APC da manyan sanatocin kasar sun bukaci Ndmume da janye wa daga takaran shugabancin gidan Majalisar don bayar da dama ga dan takaran kujerar, Sanata Ahmad Lawan.

7. APC ta bayyana dalilin da ya sa suka rasa wasu Jihohi ga Jam’iyyar PDP a zaben 2019

Jam’iyyar  shugabancin kasa, APC ta gabatar da dalilin da ya sa suka rasa cin nasarar lashe zaben wasu jihohin kasar a hidimar zaben 2019 da aka gudanar a baya.

APC sun gabatar da cewa hakan ya faru ne don sun bayar da dama ga ko wani dan Najeriya da fita takaran zabe.

8. Baban Leah Sharibu ya kamu da ciwon bugun Jini

Baban Leah Sharibu, daya daga cikin ‘yan Makarantan CHIBOK da ‘yan ta’addan Boko Haram suka sace a baya ya kamu da ciwon bugun Jini.

Naija News Hausa ta gane da cewa ‘yan Boko Haram sun saki sauran ‘yan matan da suka sace a baya, amma ba su saki Leah ba don taki amince da bukatan su.

Ka samu kari da cikakken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com

Advertisement
close button