Connect with us

Uncategorized

Barayi sun Kashe kimanin Mutane shidda a wata Harin Banki da aka yi a Jihar Ondo

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Harin da Barayi suka kai a wata Bankin Ajiyar kudi ta Jihar Ondo ya bar mutane da yawa da raunukar harbin bindiga da kuma dauke rayukan mutane kimanin mutum Bakwai.

Wasu ‘Yan Hari da Bindiga da ba a gane da su ba sun hari gidan Ajiyar kudi (Banki) da ke shiyar Isewa ta yankin Ido-Ani, a karamar hukumar Ose, Jihar Ondo.

Wannan abin ya faru ne da ranar Jiya Litini, 8 ga watan Afrilu 2019, a yayin da barayin suka fada wa bankin da hari. A nan take suka kashe Kwastomomin biyu da ke cikin bankin a yayin da suke kan cire kudi daga na’urar samar da kudi (ATM), daga nan kuma suka kashe Ma’aikatan bankin guda biyar.

Naija News ta gane da cewa barayin sun yi wa kwastomomin da suka iske cikin bankin raunuka da dama sakamakon bugu da fisga, suka kuma kwashe tullin kudi da ba mai iya bada kimanin ko nawa ne.

An bayyana da cewa barayin sun fada cikin bankin ne bayan da suka rusa ban din da wata mugun makami mai kama da bam. Suna cikin kadamar da harin su ne, sai ga rukunin Sojoji kwaram a bankin da ganawar wuta da su.

“Ko da shike har yanzu ba cikakken bayani game da lamarin” inji bayanin Kakakin Yada Labaran Jami’an Tsaron ‘Yan Sandan Jihar Ondo, Femi Joseph.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna sun gabatar a ranar Lahadi da ta gabata da yin nasara ga kashe ‘yan hari da makami biyu daga cikin wadanda suka aiwatar da mugun harin da aka yi a Kakanji, karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna a daren ranar Asabar da ta gabata.

“Ko da shike, Biyu daga cikin Jami’an tsaron mu sun sadaukar da ransu da mutuwa a ganawar wuta da maharan.” inji Yakubu Sabo, Kakakin Yada Labarai ga ‘Yan Sandan yankin.