Uncategorized
Fulani sun kai sabuwar hari a yankin Kajuru
Naija News Hausa ta karbi sabon rahoto da cewa Fulani Makiyaya sun kai sabon hari a yankin Kajuru ta Jihar Kaduna da kashe kimanin mutane fiye da Ashirin.
Naija News ta gane da cewa Kajuru na daya daga cikin yankuna da ‘yan ta’adda ke kai hari kai-da-kai a Jihar Kaduna.
Bisa bincike da rahoto da aka isar ga wannan gidan yada labaran ta mu, Abin ya faru ne a ranar Litini da ta gabata missalin karfe bakwai na maraice a kauyan Ungwan Aku ta karamar hukumar Kajuru.
Wani mazaunin shiyar ya bayyana ga manema labarai da cewa ‘yan ta’addan sun fada wa shiyar ne da harbe harbe bindiga a ko ta ina da bindigar AK47.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Kimanin mutane biyar suka rasa rayukan su a wata sabuwar harin ‘yan kunan bakin wake da aka yi a Maiduguri ta Jihar Borno a karshen makon da ta gabata.
“Da muka gane da hakan, a nan take muka fada daji da gudu. Sun shigo ne sanye da kakin Sojoji” inji shi.
Ya kara da cewa da Jami’an tsaron ‘yan sanda suka samu labarin hakan, sun haro wajen da motocin Hilux guda takwas. “amma da isar su a wajen basu iya sun bi ‘yan harin da shiga cikin daji ba”
Danladi Yarima, Tsohon shugaban Adara Development Association, ya bada tabbacin harin. Ya zargi Gwamnan Jihar Kaduna, Gwamna Nasir el-Rufai da jinkirta da kuma nuna halin makirci ga lamarin ta’addanci a Jihar.
Ko da shike a lokacin da aka bayar da wannan rahoton, ba a samu karbon bayani daga bakin DSP Yakubu Sabo ba, watau Kakakin yada yawun ‘yan sandan Jihar.