Connect with us

Uncategorized

JAMB: Hukumar Civil Defence ta bada Sharidu ga Iyaye da Masu Zama ga Jarabawan JAMB ta 2019/2020

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Kare Dama da Tsaron Al’umma, NSCDC ta Jihar Neja ta samar da Jami’an tsaron su guda 39 ga Hukumar Kadamar da Jarabawan shiga babban Makarantar Jami’a (JAMB), don tabbatar da isashen tsaro wajen jarabawan JAMB da za a yi ta shekarar bana a Jihar.

Kwamandan Hukumar ta Jihar Neja, Mista Phillip Ayuba, ya gabatar da hakan ne ga hadaddan kungiyar Manema Labaran Najeriya (NAN) a garin Minna, babban birnin Jihar Neja, a ranar Talata, 9 ga watan Afrilu ta shekarar 2019.

Ya bayyana da cewa Hukumar za ta rabas da jami’an tsaron ne ga dakunan jarabawa goma sha bakwai a cikin Jihar.

Ya ci gaba da cewa hukumar zata sanya Jami’an tsaro biyu a kowace dakin jarabawan, zata kumar sanya biyar don jagorancin dakunan jarabawa da ke a Jihar duka.

“Jami’an tsaron mu zasu tabbatar da tsaro daga farkon hidimar jarabawan har zuwa karshen hidimar jarabawan.” inji Mista Ayuba.

Mista Ayuba ya shawarci dukan wadanda zasu kasance ga zaman jarabawan da janye kansu daga halin banza, musanman kokarin satan ansa wajen jarabawa ko wata hali da bai daidanta ba.

Ya kuma yi kashaidi ga Iyaye masu taimaka wa ‘ya’yan su wajen halin makirci da magu-magu wajen jarabawa.

 

Karanta wannan kuma: Jerin Masu Arziki Goma na sama a Kannywood