Connect with us

Uncategorized

Kimanin Mutane 36 ‘yan Ta’adda suka kashe a wata sabuwar hari a Jihar Katsina

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar ‘yan Sandan Najeriya da ke a Karamar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina sun gabatar da wata hari da mahara da makami suka kai a kauyan Tsamiyar Jino, inda suka kashe kimanin mutane 14, kamar yadda aka bayar ga manema labarai.

Ko da shike mutanen kauyan sun bayar ga manema labarai da cewa lallai mutane 36 ne maharan suka kashe a harin, amma jami’an tsaro sun bayar da cewa mutane 14 ne kawai suka gano a gawakin su; Mutum bakwai daga cikin ‘yan ta’addan, mutum bakwai kuma daga cikin Hadadiyar Kungiyar ‘Yan bangan yankin da suka bayar da kansu don tsaron Kasa.
An bayar ne da cewa al’amarin ya faru ne a ranar Lahadi da ta gabata bayan da wasu ‘yan banga suka kashe wani dan ta’adda da ake ce da shi Baban Kusa.
“Wannan itace sanadiyar mayar da martani da farmaki da ‘yan ta’addan suka fado wa kauyan da hari” inji shi.

Bisa bayanin wani, ya ce “Mutane 27 aka kashe a Unguwar Rabo, Takwas kuma a Unguwar Sarkin Aiki shi kuma guda a Center Na Ade.

Wakilin Unguwa Tsamiyar Jino, Jaafaru Bello Jino ya bayar ga manema labarai da cewa kimanin mutane 36 suka mutu a sakamakon hari.

“Muna tsoron shiga daji don dauko gawakin wadanda aka kashe wajen harin don mu yi masu zana’iza a hayar da ta dace.”
“Mun kira Jami’an tsaro don sanar masu da yanazin, amma ko da suka iso, suka kuma gane da yanayin, sai kawai suka koma ba tare da wata bayani ba” inji Jino.

Kakakin Yada Yawun Jami’an tsaron ‘yan sandan yankin, SP Gambo Isah, ya gabatar da cewa maharan sun shige cikin daji da ke kewayan don buya, sun kuma tafi da gawakin ‘yan uwansu da aka kashe zuwa cikin daji.

Naija News Hausa ta tuna da cewa shugaban Jami’an ‘yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu a ranar Lahadi da ta gabata ya bada umarni ga masu haƙa ma’addinai da ke aiki a Jihar da dakatar da ayukan su, don hukumar ta samu kadamar da kame ‘yan ta’addan da ke kai hare-hare a Jihar.