Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 9 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

Published

on

at

advertisement

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 9 ga Watan Afrilu, 2019

1. Shugaba Buhari ya yi gabatarwa a wajen hidimar Taron Zuba Jarurrukar  kasa da aka yi a Dubai

Shugaban kasar Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari yayi gabatarwa a wajen Taron Zuba Jarurruka na Kowace Shekara (AIM) da aka yi a kasar Dubai, Birnin Tarayyar Kasar Larabawa (United Arab Emirate UAE) da aka yi a shakarar 2019.

Naija News Hausa ta gane da cewa shugaban yayi bayani ne akan wannan taken taro: “Zana taswirar makomar Tattalin Arzikin Harkokin Kasashen waje: Karfafa Tattalin Arzikin Duniya ta Harkokin Duniya.”

2. Filin Jirgin Sama ta Jihar Imo ta kame da Gobarar wuta

A ranar Litini, 8 ga watan Afrilu 2019 da ta gabata, gobarar wuta ya kame wajen saukan fasinjojin a filin Jirgin Sama ta Sam Mbakwe International Cargo Airport da ke a Owerri, babban birnin tarayyar Jihar Imo.

Abin ya faru ne a tsakar ranar Litini, missalin karfe biyu na ranar.

3. Ya kamata Saraki da Jam’iyyar PDP su rufe fuskan su ne don kunya – inji BMO

Kungiyar Yada Labarai na shugaba Muhammadu Buhari da aka fi sani da (BMO), sun yi wa Jam’iyyar PDP ba’a da dariya don gabatar da goyon bayan su ga tsohon babban Alkalin kasar Najeriya, Walter Samuel Onnoghen da aka gane da halin Makirci da Cin hanci da rashawa.

Naija News Hausa ta tuna da cewa Gwamnatin Tarayya a jagorancin shugaba Buhari, ta dakatar da Onnoghen ne kwanakin baya akan zargin rashin gabatar da cikakken kasafi kudi da dukiya da yake da ita.

4. Abin da dan takaran shugaban Sanatocin Najeriya, Ndume ya fada bayan ganawa da Osinbajo

Tsohon shugaban sanatocin Najeriya, Ali Ndume ya gabatar da yin watsi da jita-jitan cewa yana shirin janye daga tseren takaran kujerar shugabancin gidan Majalisar Dattijai.

Naija News ta gane da cewa Ndume ya gana ne da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a ranar Litinin da ta gabata.

5. Kotun Kara ta Jihar Rivers ta dauki mataki akan zaben Firamare na Jam’iyyar APC a Jihar

A ranar Litini da ta wuce, Kotun Kara t Jihar Rivers ta gabatar da watsi da karar da Sanata Magnus Abe ya bayar a Kotun akan zancen zaben Firamare na Jam’iyyar APC da aka yi a baya.

Babban Alkalin Najeriya, CJN Ibrahim Tanko Mohammed, ya bayyanar da cewa karar bata kai da isa abin kulawa ba.

6. Wata Rukunin Kasar Amurka ta zargi Shugab Buhari da rashin kokari akan mulki

Hukumar Yada Labarai ta kasar Amurka, Bloomberg, ta bayyana yadda shugabancin shugaba Muhammadu Buhari ya zan da mumuna tsakanin shekaru hudu da yayi akan shugabancin kasar.

Hukumar sun bayyana da cewa shugabancin Muhammadu Buhari tsakanin shekaru hudu na da alamun tawuwa.

“Wannan kuma ya bayyana da cewa shugabancin Buhari na karo ta biyu zai zamanto da mumuna bisa ta da” inji su.

7. Tsohon Kocin ‘Yan Wasan Kwallon Kafan Najeriya, Christian Chukwu na cikin Mawuyacin Hali

Christian Chukwu, Tsohon dan kwallon kafa, da kuma tsohon kocin ‘yan wasan kwallon kafa ta Najeriya na cikin mawuyacin hali na rashin lafiya.

Ko da shike ba tabbacin irin cuta da yake kame da ita, amma Naija News Hausa ta gane da cewa ana bukatar kudi Dalla $50,000 don yi masa kulawa ta gaske.

8. Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu ga bada Tallafi ga Bankin Islam

Gwamnatin Tarayyar kasar Najeriya ta rattaba hanu ga Tallafin kudi Dalla $523,823 (Milliyan N185,957,165) ga Bankin Islam (ISDB) a birnin Marrakesh ta kasar Morocco.

An gabatar da hakan ne daga bakin Ministan Harkokin Kudin Kasar Najeriya, Malama Zainab Ahmed.

9. Manyan Shugabannan Jam’iyyar APC na tsananta wa Danjuma Goje da amince da Lawan

Wasu Tsohin Gwamnonin Kasar Najeriya na tsananta wa Sanata Danjuma Goje da ya amince wa matakin da shugaba Muhammadu Buhari ya yi na goyon bayan dan takaran kujerar shugabancin Gidan Majalisar Dattijai, Ahmad Lawan.

Ko da shike akwai jita-jitan cewa shugaba Buhari ya gana da Goje akan lamarin.

Ka Samu kari da cikakken labarun kasar Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com