Connect with us

Uncategorized

PDP Jam’iyya ce da ke sauraron mutanen da suka zabe ta – Olujimi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Biodun Olujimi, Sanatan da ke Wakiltan Kuducin Jihar Ekiti, ta bayyana da cewa ba za ta janye daga Jam’iyyar dimokradiyya (PDP) ba saboda ka’idodin ta da matsayin ta na ‘yar siyasa.

Ta ci gaba da cewa Jam’iyyar PDP wata Jam’iyya ce da ke da adalci da babu irin ta cikin Jam’iyoyin kasar Najeriya.

“Wasu da suka janye daga Jam’iyyar PDP a halin yanzu suna cizon hakora da yin hakan, don ba su jin dadin inda suke” inji bayanin Olujimi a wata gabatarwa da ta yi da gidan Jaridar New Telegraph.

Da aka tambayi Olujimi ko za ta janye daga Jam’iyyar idan ta fadi ga takara, sai ta mayar da martani ta ce;

“Ni Macce ce da ke da Ka’idodi da kuma ganewa ta kwarai. Ba zani taba janye wa daga Jam’iyyar ba, dalili kuwa itace; Dole ne a san mutun da mutunci, rikon amana da kuma bayyana gaskiya.”

“A wannan Jam’iyyar ne na tara dukiyar da nike da ita da kuma samu abin zaman rayuwa. Don me zai sa in janye daga wannan Jam’iyyar da komawa ga wata Jam’iyya?”

“Ba abin da nike nema iya cika gurin mutane na da jagorancin su a hanya da ta dace, idan kuma sun ki da hakan, sai me?”

Karanta wannan kuma: Gwamna Dankwambo ya Rantse da cewa ba zai janye daga Jam’iyyar PDP ba

Ta kara da fadin cewa ba wata Jam’iyya mai adalci kamar Jam’iyyar PDP. “Jam’iyyar dimokradiyya ce da ke shirye a kowace lokaci don taimaka wa juna a kowace hanya” inji ta.

Ta karshe da gabatarda cewa Jam’iyyar na a shirye don komawa ga kan shugabancin kasar a shekara ta 2022 ta gaba.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben Kasa, INEC ta Jihar Kano ta bayar da takardan komawa ga shugabanci ga Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da Mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna da sabbin ‘yan gidan Majalisu 27.