Connect with us

Uncategorized

An Kame Barayi biyu da Kakin ‘Yan Sanda a Jihar Neja

Published

on

at

Listen to article
00:00 / 00:00

Hukumar Jami’an Tsaron ‘Yan Sandan Jihar Neja sun gabatar da kame wasu barayi biyu da ke sata da Kakin hukumar.

‘Yan Sandan Jihar sun bayyana kame dan shekaru 27, Shuaibu Pawa da abokin cin mushen sa da ke da shekaru 25, Masaudu Haruna. Rukunin ‘yan sandan na ‘Division C’ ne suka kame barayi biyun a yayin da suke aiwatar da wata hari a Ungwan Liman Madalla da ke a karamar hukumar Suleja.

Bisa rahoton da Naija News Hausa ta samu, an bayyana da cewa Shaibu da Masaudu a baya sun fada gidan wani jami’in tsaro mai suna Abdullahi Abubakar, suka kuma sace kakin aikin sa da wasu kayaki tsadar gaske da ke a gidan.

Kamfanin yada labaran ‘Northern City News’ ta gabatar da cewa barayin na cikin kadamar da sata ne a shiyar kamin jami’an tsaro suka gane da su, suka kuma kame su.

“Mu kan kadamar da hari ne da sace-sace a duk lokacin da ya gamshe mu ba tare da tsoron jami’an tsaro ba. Da yin hakan ne muke taimaka wa kanmu da zaman rayuwa” inji Masaudu.

“Wata sako ma mukan haka abu a kan hanya don sa motoci da babura yin faci. Idan hakan gurin mu kuma ya cika har motar ko baburar tayi faci, sai mu hari mai motar.”

Ya kara bayyana da cewa “mukan yi amfani da bindigar roba ne hade da muggan makamai don cin nasara ga harin mu.”

Kakakin Yada Labarai ga hukumar tsaron Jihar Neja, Muhammad Abubakar, ya bada tabbaci ga manema labarai da cewa barayin sun amince da kuma bada tabbacin cewa lallai barayin sun yarda da kuma gabatar da cewa hakan ya faru.

“Mun ribato bindigogin roba biyu, Wukake biyu da kuma Kakin hukumar mu daga hannun barayin.”

“Zamu kuma ci gaba da kadamar da bincike game da labarin.”

Karanta wannan kuma: Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Sokoto sun kame ‘yan ta’adda biyu da suka gunce hannayen wani mutumi