Uncategorized
APC/PDP: Atiku yayi Hankali, ko kuma a Jefa shi a Kurkuku – inji Lauretta

Naija News ta gano da wasu sabbin Fosta a birnin Abuja da ke dauke da hoton, Alhaji Atiku Abubakar, dan takaran kujerar shugaban kasa daga Jam’iyyar PDP ga zaben shekarar 2019.
An wallafa wasu rubutu mai zargi da alamun tanzoma a kan Fostocin. Rubutun na cewa “Na gaske da Daccece’ (The real and the right) a turance.
Fostan ya mamaye ko ta ina a Abuja, babban birnin Abuja.
Naija News Hausa ta samu wannan ne kamar yadda Lauretta Onochie, Ma’aikaciyar shugaba Muhammadu Buhari ta rabas a layin Twitter na ta da cewa ta gane da fostocin ne a isar ta a birnin Abuja ranar Talata, 9 ga watan Afrilu da ta gabata.
A bayanin ta, ta ce “Atiku ya gode ga Allah da cewa an barshi da yi yawo. Ya kamata yayi hankali da matakan sa ko kuma ya iske kansa a Kurkuku” inji ta.
Kalli sakon a kasa, kamar yadda Laurtta ta aika a layin Twitter;
I just returned to Abuja and saw @atiku‘s photos with some weird inscriptions
For one who is lucky to be walking free, whatever he is planning, he shouldnt forget that we have a President in place
Nigerians will insist that treason be treated as treason. He should counsel himself— Lauretta Onochie (@Laurestar) April 9, 2019
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Mista Niyi Akinsiju, Ciyaman na Kungiyar yada labarai ga Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana da cewa dan takaran kujerar shugaban kasa daga jam’iyyar PDP, “Atiku Abubakar na barnan lokacin shi ne da kuma lokacin kotun kara kawai.” inji shi.
“Kokarin kawai yake ya bata wa ‘yan Najeriya lokaci, shi ma ya san ba zai iya lashe zaben ba” inji su.