Connect with us

Uncategorized

Dalilin da ya sa na Amince da Karban Kaddara ga zaben 2015 – Goodluck Jonathan

 

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, ya bayyana dalilin da ya sa ya dauki kaddarar barin shugaba Muhammadu Buhari da shugabancin kasar Najeriya bisa zaben shekarar 2015 da aka gudanar a baya.

Naija News Hausa ta gane da cewa ko da shike Jonathan na da daman nuna rashin amincewa da sakamakon zaben shekarar 2015, amma tsohon shugaban bai yi hakan ba.

Jonathan, ya gabatar ne a wata zama da babban mabiya bayansa da Ma’aikacin sa, Nze Akachukwu Nwankpo, ya wakilta. Ya ce “Na dauki kaddara da sadaukar da komai da san da cewa zai amfani kasar” inji shi.

“Na gaskanta da ganin gaban kasar Africa, wannan gaban kuma zamu iya kai ga can ne idan mun gabatar da zabe a yadda ta dace a kasa. Na kuma ci gaba da kadamar da hidimar ci gaban kasa ta hanayar kafa kamfani na da na sanya wa suna “The Goodluck Jonathan Foundation” don taimaka wa dimokradiyya, zaman lafiyar kasa da kuma ci gaban kasa”

Wannan ita ce bayanin tsohon shugaban a wata gabatarwa da aka bayar a hidimar tattaunawa ta ‘OrontoNatei Douglas Memorial’ da aka yi ranar Talata da ta gabata a birnin Abuja.

Naija News Hausa ta tuna da cewa dan takaran kujerar shugaban kasan Najeriya daga Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya fada a baya da cewa “Nasara na ga zabe bai dace da zubar jinin kowa ba a Najeriya”

Wannan itace bayanin Atiku Abubakar a lokacin da ake hidimar rattaba hannu ga takardan zaman lafiyar kasa gabacin hidimar zaben shekarar 2019 da aka kamala ‘yan kwanaki da suka gabata a kasar.

Advertisement
close button