Connect with us

Uncategorized

#JAMB 2019/2019: Kalli Sharidun da ‘Yan Sanda suka bayar ga Dalibai

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Jami’an ‘yan sandan Jihar Ogun ta kalubalanci masu rubuta jarabawan shiga makarantan jami’a da
janye wa halin makirci da satar ansa ga hidimar jarabawan da za a yi a ranar 11 ga watan Afrilu 2019, kamar
yadda hukumar JAMB ta gabatar a baya.

Naija News Hausa ta sanar a baya da cewa Hukumar Gudanar da Jarabawan shiga Babban Makarantar Jami’a (JAMB)
ta gabatar da ranar rubuta Jarabawan JAMB ta shekarar 2019/2020.

Kakakin Yada Labarai ga Jami’an tsaron Jihar Ogun, DSP Bimbola Oyeyemi, ta gargadi masu zaman jarabawan a
wata ganawa da Kungiyar Manema Labaran Najeriya (NAN), a nan Jihar Ogun da cewa su janye daga halin da zai
kare dokar jarabawan a ranar jarabawa.

Bisa ganewar Naija News, kimanin mutane fiye da Miliyan N1.8m ne zasu zauna ga jarabawan daga ranar
Alhamis, 11 ga watan Afrilu ta shekarar 2019. Jarabawan zai dauki tsawon kwanaki biyu bisa sanarwan
hukumar.

“Oyeyemi ya tunatar da dalibai da cewa, binciken littafi ko amfani da wata na’ura wajen jarabawan laifi
kuma duk wanda aka gane da karya dokan jarabawan za a kama shi a kuma yi masa hukunci” inji Oyeyemi.

“Jami’an tsaro nada dama bisa doka don hukunta duk wanda suka gane da halin banza wajen hidimar jabarawan
JAMB” inji shi.

Oyeyemi ya kara da cewa Hukumar su zata samar da jami’an tsaro a kowace dakin jarabawa a Jihar don tabbatar
da tsari da kuma ganin cewa zaben ta gudana a hanyar da ta dace.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Hukumar Civil Defence ta bada Sharidu ga Iyaye da Dalibai da zasu yi Jarabawan JAMB ta shekarar 2019/2020