Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 10 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

 

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 10 ga Watan Afrilu, 2019

1. Sanata Saraki ya bada ranar karshe ga Kwamitin Gidan Majlisa da mikar da rahoton kasafin kudi ta 2019

Shugaban Sanatocin Najeriya, Sanata Bukola Saraki, a ranar Talata da ta gabata ya bayar da ranar Alhamis ta makon nan ga kwamitin gidan Majalisa da gabatar da rahoton kasafin kudin kasa ta shekarar 2019.

Shugaban ya bayyana hakan a gidan Majalisar da cewa ya bayar da ranar 11 ga watan Afrilu ga Majalisar da mikar da kasafin kudin shekarar, gabacin ranar 16 ga watan Afrilu da za a rattaba hannu da kuma gabatar da amince da kasafin kudin.

2. Gidan Majalisa ta gabatar da Ciyaman na Kungiyar NEDC

A ranar Talata da ta wuce, gidan Majalisar Dattijai ta gabatar da Maj. Gen. Paul Tarfa (rtd.) a matsayin sabon ciyaman na Kungiyar Ci gaba ta Arewa maso Gabashin kasar Najeriya (NEDC).

Gidan Majalisar ta kuma gabatar da sanya Mohammed Alkali a matsayin Darakta na Kungiyar da jagorancin mambobin Kungiyar guda goma.

3. Majalisar Dattijai ta rattaba hannu da gabatar da Tallafin Kudi ga Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya

A ranar 9 ga Watan Afrilu, Talata da ta gabata, Gidan Majalisar Dattijai sun gabatar da amince da hidimar Tallafin kudi ga Jami’an tsaron ‘yan sandan kasar Najeriya.

Majalisar ta yi hakan ne don cika alkawarin da shugaban sanatoci, Dakta Abubakar Bukola Saraki yayi ga shugaban ‘yan sandan kasar Najeriya, IGP Mohammed Abubakar Adamu, na cewar zai tabbatar da cewa bai jinkirta da gabatar da hidimar tallafin hukumar ba.

4. Kungiyar ASUP na Barazanar komawa ga Yajin Aiki

Hadaddiyar Kungiyar Malaman Makarantar Fasaha (ASUP), na barazanar cewa zasu koma ga yajin aikin da suka dakatar a baya ganin cewa Gwamnatin Tarayya ba ta cika alkawalan su ga Kungiyar ba.

Naija News Hausa ta tuna da cewa wannan matakin ya biyo ne bayan watannai biyu da ta gabata da kungiyar ta dakatar da yajin aikin da suka soma a baya. Sun yi hakan ne don isa ga amincewa da Gwamnatin Tarayya.

5. ‘Yan Sandan Najeriya sun dakatar da Ofisoshi 9, da kuma rage Igiyar wasu 6 kuma

Hukumar Jami’an Tsaron Najeriya (NPF), a ranar Lahadi da ta gabata sun gabatar da tsige Manyan Ofisoshi 9 da kuma rage Igiyar daraja ga Ofisoshi  6 akan wasu laifuka.

Naija News Hausa ta gane da cewa Hukumar tayi hakan ne bayan wata ganawar da Jami’an tsaron suka yi a birnin Abuja, ranar 26 ga watan Maris 2019, bisa bayanin Kakakin Yada Yawun Hukumar tsaron, Ikechukwu Ani.

6. Ba zan taba Janye daga Jam’iyyar PDP ba –  inji Sanata Olujimi

Biodun Olujimi, Sanatan da ke Wakiltan Kuducin Jihar Ekiti, ta bayyana da cewa ba za ta janye daga Jam’iyyar dimokradiyya (PDP) ba saboda ka’idodin ta da matsayin ta na ‘yar siyasa.

“Wasu da suka janye daga Jam’iyyar PDP a halin yanzu suna cizon hakora da yin hakan, don ba su jin dadin inda suke” inji bayanin Olujimi a wata gabatarwa da ta yi da gidan Jaridar New Telegraph.

7. Yakamata Mataimakin Gidan Majalisa ya fito ne daga Kudu Maso Gabashin kasar – inji Kalu

Orji Uzor Kalu, Tsohon Gwamnan Jihar Abia, ya gabatar da cewa ya kamata ne mataimakin shugaban Gidan Majalisar Dattijai ya fito daga Kudu Maso Gabashin Kasar Najeriya.

Sanata Kalu, ya fadi hakan ne da cewa yin hakan zai taimaka wajen dai-daita shugabanci a kasar ba tare da nuna banbanci ba.

8. Ya kamata Majalisar Dattijai su Kalubalanci Gwamnatin Buhari – PDP

An shawarci Gidan Majalisar Dattijai da yin kira da Kalubalantar Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da are-aren kudade daga kasashen waje ba tare da wata manufan kwarai ba.

Naija News Hausa ta sanar da cewa Jam’iyyar Dimokradiyya, PDP ne ta shawarci Gidan Majalisar Dattijai da yin hakan.

Ka samu kari da cikakken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com

Advertisement
close button