Uncategorized

A yau Alhamis, 11 ga watan Maris 2019, Gwamnatin Tarayya ta gabatar da ranar da za a biya Ma’aikatan N-Power albashin su na watan Maris.
Hukumar da ke jagorancin N-Power ta gabatar da ne da hakan daga bakin Mista Afolabi Imoukhuede, Babban Mataimakin shugaba Muhammadu Buhari wajen kirkiro ayuka ga Matasan kasar Najeriya.
Mista Imoukhuede ya gabatar ne a birnin Abuja a yau Alhamis, 11 ga watan Maris da cewa Gwamnatin Tarayya zata biya albashi ga Ma’aikatan N-Power a cikin wannan makon. Bisa bayanin Imoukhuede ga Kungiyar Manema Labaran Najeriya (NAN) a birnin Abuja.
Naija News Hausa ta gane da cewa ma’aikata na kuka da fusata da rashin karban albashin su na watan Maris da ta gabata.
Imoukhuede ya bayyana da cewa rashin biyar albashin ma’aikatan N-Power ya faru ne bisa wata matsala da Hukumar ta fuskanta da Ofishin Hukumar Kula da Tattalin Arzikin kasa. Ya kara da cewa an riga an magance matsalar kuma za a biya albashi ga ma’aikata a wannan makon.
Ya kuma bayyana watsi da zargin da ake yi na cewar Hukumar ta biya Baji na biyu ne da manta da Baji na Biyu.
“Ba gaskiya bane, Hukumar bata biya wani Baji ba, ko kuma nuna wata banbanci ba ga Ma’aikata. Matsala ne kawai aka samu kuma Gwamnatin Tarayya ta magance wannan.” inji shi.
“Ina da tabbacin cewa kowa zai yi murmushi a wannan makon, saboda na magance matsalar kuma za a biya kudi ga ma’aikata” inji Mista Afolabi.
Karanta wannan kuma: Barayi sun Kashe kimanin Mutane shidda a wata Harin Banki da aka yi a Jihar Ondo