Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 11 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

Published

on

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 11 ga Watan Afrilu, 2019

1. Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya sa yake ‘Baba Go Slow’

Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da martani game da sunan da aka laka masa na ‘Baba Go Slow’

A wata zaman tattaunawa da shugaban ya halarta da ‘yan kasan Najeriya da ke a Dubai, shugaba Buhari ya ce “Na amince da sunan ‘Baba Go Slow’ amma dai ni ba na satan kudi daga asusun kasa.” inji shugaban.

2. Kotun Koli ta Jihar Kwara tayi watsi da karar dakatar da Balogun-Fulani

Kotun Koli ta gabatar da yin watsi da karar da wata rukuni ke yi na zancen neman a dakatar da mai suna, Shugaban Fulani da aka fi sani da ‘Balogun Fulani’ a jagorancin jam’iyyar APC ta Jihar Kwara.

Rukunin mutane biyar daga kotun ta gabatar ne da hakan a yau, Alhamis, da yin watsi da karar bisa gane da cewa karar bai isa abin kulawa ba.

3. Alkalin da ke jagorancin karar Okorocha ya janye kansa daga karar

Alkalin Kotun Kolin Tarayyar kasa, Mista Taiwo Taiwo, da ke jagorancin karar da ke tsakanin Hukumar INEC da tsohon gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, ya janye kansa daga karar bayar da takardan komawa kan kujerar mulki bisa zaben da aka yi a baya a Jihar Imo.

Naija News Hausa da gane da cewa Rochas na kalubalantar Hukumar INEC ne da rashin bayar da tarkadan kujerar Sanatan Jihar Imo a gareshi, bisa ya lashen zaben.

4. Atiku ya yi bayani game da zancen hada kai da ‘yan kasar Waje don tsige Buhari

Dan takaran kujerar shugaban kasar Najeriya ga zaben 2019 daga Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, yayi watsi ga zargi da kuma jita-jita da ake na cewar ya hada kai da ‘yan kasan US (Amurka) don tabbatar da tsige shugaba Muhammadu Buhari daga kujerar shugabancin kasa.

Naija News ta gane da wata rahoto a ranar Talata da ta gabata da ke cewar, Atiku Abubakar ya bayar da kudi kimanin Dalla $30,000 don hada kai da ‘yan kasar US don tabbatar da cewa Buhari bai ci nasara ga zaben 2019 ba.

5. Hukumar IMF ta Gargadi Najeriya da sauran Kasashe game da aron kudi daga China

Hadaddiyar Hukumaf Samar da Kudi ga Kasashe (IMF), ta Gargadi kasar Najeriya da sauran kasashe da ke tasowa da janye kansu daga neman aron kudi daga kasar China, don ganin yawar neman riba da kasar China ke yi wajen samar da aron kudin su.

Hukumar ta gabatar ne da wannan gargadin daga bakin Mista Tobias Adrian, a ranar Laraba a wata ganawa da hukumar suka yi a birnin Washington D.C.

6. Birnin Ilori da Port Harcourt na fuskantar rashin Man Fetur

Bisa ganewa da kuma dogon layi da daya daga cikin Ma’aikacin Naija News Hausa ya dandana a ranar Jiya da Yau, Mun iya gane da cewa rashin Man Fetur ya bayyana a birnin Ilorin ta Jihar Kwara da kuma babban birnin Jihar Rivers, Port Harcourt.

Gidan Yada Labaran mu ta gane da cewa yawancin gidan mai da ke a biranen sun kulle kofar shiga gidan Mai nasu. Wannan alamu ce na rashi da tsadar man fetur.

7. Atiku yayi watsi da sabbin Fostocin da aka manna a ko ta ina a birnin Abuja

Dan takaran kujerar shugaban kasan Najeriya na Jam’iyyar PDP ga zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana yin watsi da wasu Fostoci da ke dauke da hoton sa, da aka manna ko ta ina a birnin Abuja.

Naija News Hausa ta ruwaito  a baya da cewa Lauretta Onochie, Ma’aikaciyar shugaba Muhammadu Buhari ta rabas a layin Twitter na ta da cewa ta gane da wasu fostoci da ke dauke da hoton Atiku, da kuma wasu rubutu da ke da alamun tada tanzoma.

8. Shugaban Hukumar ‘Fire Service’ na Jihar Legas ya samu yanci daga hannun ‘yan hari

Mista Rasaki Musibau, Shugaban Hukumar Yaki da Gobarar Wuta (Fire Service) na Jihar Legas, hade da wasu mutane shidda da ‘yan hari da makami suka sace a ranar Asabar da ta gabata sun samu yanci.

Shafin Naija News ta turanci ta sanar a baya da cewa ‘Yan hari sun sace Mista Rasaki da wasu mutane a Jihar Legas.

9. Kada Iyamira (Igbo) su zata ko Buhari zai taimaka masu da komai a shugabancin shi ta biyu – Okorocha

Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, ya gabatar ga ‘yan Iyamiran duka da yin watsi da duk wata tunani ko zaton cewa shugaba Muhammadu Buhari zai taimaka masu ga shugabancin sa na karo biyu, don basu zabe shi ba, inji shi.

Okorocha ya gabatar ne da hakan a wata ganawa da yayi da manema labarai a birnin Owerri.

Ka samu kari da cikakken labarun Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com