Uncategorized
PDP/APC: Bani da wata liki da sabbin Fostocin da aka mamaye birnin Abuja da ita – Atiku

Alhaji Atiku Abubakar yayi watsi da zargin manna wasu sabbin Fostoci a birnin Abuja
Dan takaran kujerar shugaban kasan Najeriya na Jam’iyyar PDP ga zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana yin watsi da wasu Fostoci da ke dauke da hoton sa da aka manna ko ta ina a birnin Abuja.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Lauretta Onochie, Ma’aikaciyar shugaba Muhammadu Buhari ta rabas a layin Twitter na ta da cewa ta gane da wasu fostoci da ke dauke da hoton Atiku, da kuma wasu rubutu da ke da alamun tada tanzoma.
A bayanin Lauretta game da fostan Atiku, ta ce “Atiku ya gode ga Allah da cewa Gwamnatin Tarayya a jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta bashi daman yawo yadda ya ga dama. Ya kamata yayi hankali da matakan sa ko kuma ya iske kansa a Kurkuku” inji ta.
A wata sanarwa da aka bayar a ranar Laraba da ta gabata daga bakin Peter Ibe, Mai bada shawarwari ga, Atiku Abubakar, ya bayyana da cewa bai da wata liki da wannan fostan.
Naija News Hausa ta gane da cewa Fostan da ake zargin Atiku da ita na dauke ne da wasu rubutu da ke da alamun zargi da tayar da tanzoma, musanman karya dokar kasa bisa an gabatar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mai nasara ga hidimar zaben 2019.
Fostan ya bayyana Atiku a matsayin ‘Wanda ya dace da mulki’ da kuma ‘Na Ainihi’.
An kuma rubuta abin da yaren Indiya ‘Pukka’ ma’ana a turance ita ce “authentic, genuine, sure, solid and excellent.” watau ‘Wanda ya dace da mulki’ da kuma ‘Na Ainihi’.
Bisa bincike da ganewar Kungiyar Maneman labaran Najeriya (NAN), an gano da fostocin kuma a Yola, babban birnin Jihar Adamawa.
Daraktan Kungiyar Yaki da Daman Atiku ga zaben 2019, Sani Adamu, ya bayyana da cewa rukunin da ta yi wannan ba ta da manufa ko shirin tayar da hankali ko tanzoma a kasar, kuma bai zata da cewa sun karya dokar Hukumar INEC ba bisa zaben kasa.
“An jawo hankalin mu da wasu fostoci a birnin Abuja da ke dauke da hoton Atiku Abubakar, dan takaran shugaban kasar Najeriya daga Jam’iyyar PDP ga zaben 2019.”
“Muna watsi da wannan liki da zargi ga dan takaran mu. Lokacin yaki ga neman zabe ya wuce. Mun kuma riga mun gabatar da rashin amincewar mu da sakamakon zaben a Kotun kara bisa dokar zabe”
“Ba zamu kauce daga gurin mu ba, mun gane da cewa wannan itace bukatar Jam’iyyar adawan mu, ba zamu kuma raunana da neman ribato daman mu ba” inji Ibe.
Mista Ibe ya bayyanar da hakan ne ga manema lanaran NAN da cewa babu ruwan Atiku da wannan fostan.
“Ban sa wannan fostan a ido ba. A gareku na ke jin hakan. Bamu san da su ba, kuma bamu da wata liki da hakan” inji shi.
Karanta wannan kuma: Tsohon shugaban Kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya bayyana dalilin da ya sa ya dauki kaddara ga zaben 2015