Connect with us

Uncategorized

An Gabatar da Kasafin kudi na naira Biliyan N139b ga Gidan Majalisar Tarayyar kasar Najeriya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Alhamis, 12 ga watan Afrilu 2019, Shugabancin Gidan Majalisar Tarayyar kasar Najeriya ta bayyana kasafin kudin gidan Majalisar ta shekarar 2019.

Naija News Hausa ta gane da cewa wannan matakin ya biyo baya ne bisa umarni da shugaban Sanatocin kasar, Sanata Bukola Saraki ya bayar ‘ga gidan Majalisai da mikar da kasafin kudin su a gaban gidan Majalisar kamin ranar yau, 12 ga watan Afrilu.

Majalisar ta gabatar da hakan ne a layin yanar gizon nishadarwa ta Twitter na shugabancin Gidan Majalisar, a yau Jumma’a.

Wannan kudin bisa ga yadda aka wallafa shi, za a rabar da shi ne tsakanin Gidan Majalisar Dattijai, Majalisar Wakilan Jihohi, Ma’aikatan Gidan Majalisar Dattijai da ta Wakilai duka, hade da wasu hanyoyi kuma da aka bayyana na amfani da kudin.

Kalli sakon a layin Twitter a turance;