Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 12 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 12 ga Watan Afrilu, 2019

1. Ku ci Mutuncin ‘Yan Ta’adda da Barayi-Buhari ya gayawa Hukumomin Tsaron kasa

Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarni ga Hukumomin tsaron kasar Najeriya duka da su ci mutuncin ‘yan ta’adda, mahara da barayi, da kuma magance matsalar tsaron kasar Najeriya.

Naija News ta gane da hakan ne a bayanin Shugaban Hukumomin Tsaron Kasar, Gabriel Olonisakin, ya bayar bayan ganawar tsawon awowi biyu da aka yi da shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis da ta gabata a Fadar Shugaban Kasa da ke a birnin Abuja.

2. Gwamnatin Tarayyar Kasa ta mayar da Martani game da bashin da Najeriya ta ci

A ranar Laraba da ta gabata, Kungiyar Shugabannan Tarayyar Kasa (FEC) ta gabatar da cewa kada al’ummar kasa su ji tsoro game da bashin da kasar ke ci.

“Kada ku ji tsoro kan bashin da shugabancin kasar ke ci, kasar na da karfin biyan duka” inji Kungiyar, a bayanin Ministan kasafin kudin kasa, Udoma Udo Udoma, a gabatarwan da yayi ga wata taro da suka yi a jagorancin mataimakin shugabana kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

3. Kotun Kara tayi watsi da karar Jam’iyyar APC a Jihar Rivers

Kotun ta gabatar da watsi da karar da Jam’iyyar APC ta Jihar Rivers ta mika a gaban kotun. Da fadin cewa karar bai taka kara da karewa ba.

Kotun ta bayyana hakan ne bisa shari’ar da babban shugaban Alkalan kasar, Alkali Tanko Mohammed ya gabatar.

4. Gwamnatin Tarayya ta Gargadi Atiku

A ranar Alhamis da ta gabata, Gwamnatin Tarayya ta bada gargadi ga dan takaran kujerar shugaban kasa daga Jam’iyyar PDP, Alh. Atiku Abubakar, da cewa ya bar Kotun Kara da bayyana shari’a da kuma matakin su game da sakamakon zaben 2019 da aka yi a ranar 23 ga watan Fabrairun.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa an gano wasu sabbin Fostoci a birnin Abuja da ke dauke da hoton Atiku Abubakar da kuma rubutu da ya bayyana Atiku a matsayin shugaban da ya dace ga kasar.

5. Hukumar EFCC ta saki Ubani daga kulle

A ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu da ya gabata, Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da kare Tattalin Arzikin Kasa, EFCC ta saki tsohon mataimakin shugaban Kungiyar Alkalan kasar Najeriya (NBA), Monday Ubani.

Naija News Hausa ta tuna da cewa Hukumar ta kame Monday Ubanyi da Sanata Christopher ne a ranar 19 ga watan Maris da ya gabata, akan wata zargi.

6. Tsohon shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana hanyar da kasar zata samu zaman Lafiya

Tsohon shugaban kasar Najeriya da kuma Ciyaman na Kamfanin ‘Goodluck Jonathan Foundation (GJF), Dakta Goodluck Jonathan ya bayyana da cewa kasar Afrika za ta iya samun zaman lafiya ne kawai idan an bada dama ga bayyanar shugabancin Dimokradiyya.

Jonathan ya gabatar da hakan ne a birnin Yenagoa, a ranar Alhamis da ta gabata, lokacin da Dakta Stephen Olali ya ziyarce shi a Jihar Bayelsa.

8. An tsige shugaban Kasar Sudan, Omar Al-Bashir daga shugabancin kasar

Naija News ta samu tabbacin cewa kasar Sudan ta tsige shugaban kasar su, Omar Al-Bashir,  a ranar Alhamis da ta gabata. suna kuma kadamar da shirin sanya sabon shugaba.

Naija News Hausa ta gane da cewa shugaba Omar ya shugabancin kasa Sudan da tsawon shekaru kusan 30.

9. Majalisar Wakilai sun ba shugaba Buhari tsawon awowi 48 da bayyana a gidan majalisar

Gidan Majalisar Wakilan Jiha sun bukaci shugaba Muhammadu Buhari da bayyanar da kansa a zaman Majalisar don gabatar da sanadiyar kashe-kashen da ake yi a Jihohin kasar.

Majalisar ta bada daman awowi 48 ne kawai ga shugaban da yin hakan.

Ka samu kari da cikakken labaran kasar Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com