Connect with us

Uncategorized

Sarakan Jihar Zamfara na zargin Rundunar Sojojin Sama da kashe mutane a banza

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kungiyar Sarakan Jihar Zamfara sun gabatar da wata zargi da cewa rundunar sojojin sama ta Najeriya sun kure aika bama-bamai ga ‘yan ta’adda.

Zargin na cewa “Rundunar Sojojin Sama sun hari mutanen Jihar da bama-bamai maimakon ‘yan ta’adda.”

Kungiyar Sarakan sun gabatar da zargin ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Alhamis da ta gabata a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru ya gabatar a bayanin sa da cewa Rundunar Sojojin sun aika bama-bamai a wasu shiyar da ba ‘yan ta’adda ke ciki ba.

“Rahoton ta aka bayar game da nasarar rundunar sojojin, musanman a yankin Mutu ta karamar hukumar Gusau, Tsafe, Tangaram da karamar hukumar Anka da yankin Dumburum ta karamar hukumar Zurmi ba gaskiya bane”

“Wadanda aka kashe a yankunan nan ba ‘yan ta’adda bane” inji Sarki Attahiru.

“Idan da ace ‘yan ta’adda ne aka kashe a wadannan hare-haren, da lallai harin ya hana sauran ‘yan ta’addan motsi. musanman samu fita, sayan abinci ko neman kayan rayuwa a kangin su”

Karanta wannan kuma: Hukumar Jami’an Tsaron ‘Yan Sandan Jihar Neja sun gabatar da kame wasu barayi biyu da ke sata da Kakin hukumar.