Uncategorized
Gobara ya kone mutane 12 har ga Mutuwa a wata Hadarin Motar Tanki
Kimanin Mutane Goma shabiyu suka kone kurmus da wuta a wata gobarar wuta da ya faru a Jihar Gombe.
Hakan ya faru ne bayan wata gobarar wuta da aka yi sakamakon wata hadarin motar Tanki da ke dauke da Man Fetur a ranar Asabar da ta gabata.
Mutanen shiyar sun yi rashin Gidajen su da kayaki, da kuma raunuka da dama a yayin da gobarar wutan Tankin ya ratsa ga mazaunin shiyar.
Bisa bayanin wani da ke da sanin yadda abin ya faru, ya ce “Gobarar ta faru ne bayan da wata Motar Tankin ta hade da wata Babbar Mota da ke dauke da ruwar kwalba a hanyar baifas ta garin Gombe, a gaban wata Gidan Mai”
Ya kara da cewa ‘yan Kungiyar ‘Nigerian Red Cross’ da wasu ma’aikata da ke shiyar suka taimaka ga kashe yaduwar wutan da kuma tsamo gangar jikin wadanda wutar ya kone har ga mutuwa.
“Hadarin Motar Tankin da Babban Motar da ke dauke da ruwan kwalba ya faru ne a missalin tsakar ranar Asabar a gaban wata gidan mai” inji Mazaunin.
Ko da shike a lokacin da aka karbi wannan rahoton, ba a samu karban bayani daga Jami’an tsaro da Hukumar Road Safety ba.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa mutane uku sun kone kurmus da wuta sanadiyar wata hadarin mota da ta faru a wata Gidan Man fetur da ke a yankin Okene ta Jihar Kogi.