Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 15 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

 

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 15 ga Watan Afrilu, 2019

1. Karya ne, babu rashin Man Fetur a kasar – inji Kachikwu

Ministan Man Fetur na Jihohin kasar Najeriya, Ibe Kachikwu ya gabatar ga ‘yan Najeriya a ranar Lahadi da ta gabata da cewa akwai isashen man fetur a kasar.

Naija News Hausa ta gane da cewa Kachikwu ya fadi hakan ne don mayar da martani ga zancen rashin yaduwar man fetur da ake fuskanta a wasu Jihohin kasar.

2. Biafra sun mayar da martani zancen APC na cewar Atiku ba dan Najeriya ba ne

Kungiyar ‘yan Biafra (IPOB), sun mayar da martani akan bayanin ‘yan Jam’iyyar APC na cewar Alhaji Atiku Abubakar ba dan kasar Najeriya bane.

Kungiyar ta ce, lallai bayanin Jam’iyyar APC ya goyi bayan bayanin da shugaban kungiyar su, Nnamdi Kanu yayi ne a baya na cewar Atiku dan kasar Kamaru ne.

3. Karya ne ban gana da Gwamnonin Jam’iyyar PDP ba – inji Lawan

Shugaban Sanatoci daga Jam’iyyar APC, Ahmed Lawan yayi watsi da zancen da ake da shi na yin ganawa da Gwamnoni Jam’iyyar PDP don neman kujerar shugabancin gidan Majalissai.

Lawan ya gabatar da rashin amince da zargin ne a bakin Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, Kakaki da jagoran yakin neman kujerar shugabancin gidan majalisar gan dan takaran.

4. Jam’iyyar PDP ta lashe zaben Gidan Majalisun Jihohi duka

Bisa zaben Gidan Majalisun Jihar Rivers da aka sake yi, Jam’iyyar PDP ta Jihar ta lashe zaben Jihar duka.

Naija News Hausa ta gane da cewa PDP ta lashe zabunan da aka yi a kananan hukumomin Jihar guda hudu; watau Karamar hukumar Gokana, Karamar hukumar Abua/Odual, Ahoada Kudu, da kuma Opobo/Nkoro.

5. Dalilin da ya sa Lauyan Atiku ba zai iya aiki a kasar Najeriya ba – INEC

Hukumar Gudanar da Hidimar zaben Kasar Najeriya, INEC ta gabatar da cewa Lauyan Atiku Abubakar, dan takaran Kujerar shugaban kasa daga Jam’iyyar adawa (PDP) ba zai iya yin aikin sa na Lauyanci ba a kasar Najeriya, saboda ba a bashi yancin yin hakan ba a kasar Najeriya.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Atiku Abubakar ya gabatar da karar rashin amincewa da gabatar da Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya, bisa zaben da aka yi a watan Maris ta 2019 da ta gabata.

6. Sanata Ekweremadu, Dino Melaye da Akinyelure na neman shugabancin Gidan Majalisar Dattijai ta kasa

Sanatoci Ukku daga Jam’iyyar PDP ke neman shugabancin karamar hukumar Gidan Majalisai a shafin zaben shugabannan Gidan Majalisa ta tara da ke a gaba.

Na farko a takaran shi ne Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban gidan Majalisa ta da, na biyu kuma shine Sanata Dino Melaye (Daga Kuduncin Jihar Kogi) da kuma Sanata Ayo Akinyelure daga Jihar Ondo.

7. Atiku bai kadamar da makirci don rashin ci gaban Buhari – inji Paul Ibe

Mai bada Shawarwari ta fanin yadarwa ga dan takaran kujerar shugaban kasa daga Jam’iyyar PDP, Paul Ibe ya bayyana da cewa Atiku Abubakar bai kadamar da wata shirin makirci don tsananta wa shugabancin Buhari.

Ibe ya fadi hakan ne don mayar da martani akan wasu jita-jita da Jam’iyyar ta gane da ita.

Ka samu kari da cikakken labaran kasar Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com

Advertisement
close button