Connect with us

Uncategorized

Rundunar Sojoji sun ci nasara da kashe ‘yan Boko Haram 27

Published

on

at

Rundunar Sojojin Najeriya da ta Kamaru sun yi nasara da kashe ‘yan ta’addan Boko Haram 27 a wata ganawar wuta.

Naija News ta samu tabbacin hakan ne a wata ganawa da Col. Sagir Musa, Kakakin yada labaran Hukumar yayi da manema labarai a yau Litini.

Bisa bayanin Mista Sagir, Rundunar Sojojin sunyi ganawar wuta ne da ‘yan ta’addan a Arewacin Wulgo, Tumbuma, Chikun Gudu, da Kauyan Bukar Maryam.

Ya bayyana da cewa Rundunar Sojojin Najeriya da ta Kamarun da basu samu wata rauni ko rasa wani ba a ganawar wutar.

“Sojojin a bayan da suka yi nasara da ‘yan ta’addan sun kuma samu ribato Mugayan Makamai da bindigogi kamar su, AK 47, Bindigar G3, da wata na’urar bama-bamai” inji Musa.

Ya kara da cewa Rundunar Sojojin na kara karfafa da kuzari don ganin cewa sun ci gaba da yin nasara da ‘yan ta’addan da ke a shiyar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Tsohon Leah Sharibu, daya daga cikin yaran makarantar Dapchi da ‘yan ta’addan Boko Haram suka sace a baya, ya kamu da ciwon bugun jini.

Hakan ya bayyana ne a yayin da wakilan yankin Chibok da Dapchi suka gabatar a ziyarar su ga Annabi Temitope Joshua da aka fi sani da suna TB Joshua, shugaban wata babban Ikklisiya ta Jihar Legas da aka fi sani da Synagogue Church of All Nations.

Naija News Hausa tunani da duban cewa watakila Mista Nathaniel Sharibu, baban Leah ya kamu ne da rashin lafiyar watakila don yawar tunanin diyarshi.

Karanta wannan kuma: Ba zaka iya zama Shugaban Kasa ba ta bin Kofar baya – APC ta gayawa Atiku