Labaran Najeriya
Shugabancin Buhari ba ta da wata Unfani ga kasar Najeriya – Ango Abdullahi
Kakakin Yada yawun Kungiyar Manyan Masu fadi a Ji ta Arewancin kasar Najeriya (Northern Elders Forum, NEF), Ango Abdullahi ya yafa yawu da bayyana kasawar shugabancin shugaba Muhammadu Buhari bisa kashe-kashe da ke gudana a kasar.
A bayanin Abdullahi, ya fada da cewa kasar Najeriya na cikin mawuyacin halin rashin tsaro, musanman Arewancin kasar.
“Kasar Najeriya na fuskantar rashin tsaro, wannan kuma ya bayyana kasawar shugabancin Muhammadu Buhari.” inji shi.
Abdullahi ya kalubalanci shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnatin sa da nuna kulawa ta gaske wajen magance matsalar tsaro da ake ciki a kasar, musanman a Jihohin Arewa kamar; Zamfara, Katsina, Kaduna, Benue, Niger, Plateau da Jihar Taraba.
“Shugabancin kasar Najeriya ta kasa ga jagorancin ta. Ta kasa ga samar da tsaro a kasa, ta kasa ga gyara tattalin arzikin kasa, talauci ya hau bisa ga da a kasar, musanman a Arewacin kasar”
“Mun kira ga Gwamnatin da daukar matakai da zasu karfafa tattalin arzikin kasar. Matakan da zasu kawo ci gaba a kasa”
Abdullahi ya kara da cewa kasar na fuskantar mugayan hare-hare daga ta’addan Boko Haram, Mahara masu sace mutane, ‘yan hari da makami, dadai ire-iren mugayan hari.
“Maimakon Arewa ta ci gaba sai raunana da komawa baya ta ke yi.” inji.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Gidan Majalisar Wakilan Jiha sun bukaci shugaba Muhammadu Buhari da bayyanar da kansa a zaman Majalisar don gabatar da sanadiyar kashe-kashen da ake yi a Jihohin kasar.