Connect with us

Uncategorized

‘Yan Ta’adda sun kashe yaron wani Jigon Jam’iyyar PDP a Jihar Benue

Published

on

at

advertisement

Hukumar Jami’an ‘yan Sandan Jihar Benue ta gabatar da yadda ‘yan ta’adda suka sace Orkuma Amaabai, yaron wnai Jigon Jam’iyyar PDP a Jihar Benue, dan Sarki Yandev Amaabai.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne a wata sanarwa da Kakakin Hukumar ‘yan sandan Jihar, PPRO, DSP. Ms Catherine Anene ta bayar ga Kungiyar manema labaran kasar Najeriya (NAN) a ranar Lahadi da ta gabata a birnin Makurdi, da cewa ‘yan ta’adda sun harbe Orkuma ne a shiyar Gboko, missalin karfe 10 na daren ranar Asabar da ta gabata.

DSP Anene ta bayyana da cewa hukumar su na kan bincike akan lamarin. Ta kuma shawarci mutanen Jihar da bayar da duk wata alamu da zai kai ga gane mafari da kuma wadanda suka aiwatar da mugun harin.

Ya kuma bayyana da cewa Dan Matashin da aka kashe, Orkuma, dan farko ne ga Iyayen sa.

Babban Sakataren yadarwa na Jam’iyyar PDP ta Jihar Benue, Mista Bemgba Iortyom, ya bayyana abin a matsayin abin takaici. Ya karfafa jami’an tsaro da yin kokarin kame wadanda suka aiwatar da kisan Orkuma.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa ‘yan matan Boko Haram biyu sun fashe da Bam a yayin da suke kokarin isa wata shiyya a kauyan Monguno.

Soja daya da Dan banga daya aka rasa a wannan tashin bam din, hade da ‘yan kunar bakin waken.