A Karshe Npower ta fara biyan Ma'aikata Albashin watan Maris | Naija News Hausa
Haɗa tare da mu

Labarai Hausa

A Karshe Npower ta fara biyan Ma’aikata Albashin watan Maris

Published

Bayan ‘yan kwanaki kadan da ma’aikata ke kukan cewa ba a biya su albashin watan Maris ba, a halin yanzu mun sami tabbaci a Naija News Hausa da cewa Hukumar NPOWER a jagorancin Gwamnatin Tarayya ta fara biyar ma’aikata albashin watan Maris da ta gabata.

Mun gane da hakan ne a wata sanarwa da wani daga cikin Malaman Aikin Npower ya bayyanar ga manema labarai..

Albashin, na naira dubu Talatin (30,000) ya biyo ne ‘yan kwanaki kadan da gabatowan Hidimar Bikin Easter. Wannan zai taimaka sosai musanman ga ‘yan addini Kirista don samun biyan wasu bukatun su na gida ko don tafiya.

 

Karanta wannan kuma: Abdulrahman yayi Barazanar Kashe Kadaria Ahmed don janyewa daga Musulunci

 
Kuna iya aika Naija News ta hanyar amfani da maɓallin rabar mu. Aika duk labarai da sake bugawa zuwa [email protected].