Jirgin Kasa ya take Mutane biyu a Jihar Kano

Hukumar ‘yan sandan Jihar Kano ta gabatar da mutuwar wasu mutane biyu da Jirgin Kasa ta take a yau.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne a wata sanarwa inda DSP. Abdullahi Haruna, Kakakin yada yawun hukumar ‘yan sandan Jihar ya bada tabbacin hakan.

DSP Haruna ya bayar da cewa abin ya faru ne yau safiyar ranar Talata, 16 ga watan Afrilu a missalin karfe Takwas na safiya, inda Jirgin Kasa ya take wasu mutane biyu da ba a gane sunansu ba.
Hakan ya auku ne a hanyar jirgin kasa da ke a shiyar hanya da ta bi bayan Kano Club, a karamar hukumar Nasarawa ta Jihar Kano.

“A lokacin da Jami’an tsaro suka isa wajen, sun gane da cewa Jirgin kasan ya guntse daya daga cikin mutanen biyu, ya rabar da gangar jikinsa biyu.” inji bayanin Haruna.

Ya kara bayyana da cewa an riga an kai gawar jikunan a wata asibiti da ke a cikin Jihar. Ya kuma gargadi mutane da janye wa hanyar Jirgin Kasa don gujewa irin wannan mumunar abin da ya faru da mutane biyun da Jirgin saman ya take.

Naija News Hausa ba ta iya gane Suna, Shekaru ko Jintsin mutanen da Jirgin Kasan ya take ba a lokacin da aka karbi wannan rahoton, saboda ba a bayar da hakan ba.
Duk da hakan ana kan bincike akan lamarin, idan akwai wata karin bayani da ya biyo baya, zamu sanar a nan.

Karanta wannan kuma: Gobara ya kone mutane 12 har ga Mutuwa a wata Hadarin Motar Tanki