Connect with us

Uncategorized

Kalli dalilin da ya kai Wani dan Shekara 12 da shan Gamale a Jihar Kogi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilu da ta gabata, wani dan shekara goma shabiyu (12) a Jihar Kogi ya sha maganin kashe kwari da aka fi sani da (SNIPER) don gujewa tsawatawar yayar shi.

Yaron da aka gane da suna Bobo, ya sha maganin kashe kwarin ne bayan da yayar sa ta tsawata masa akan wata laifi da yayi.

Bisa bayanin da aka bayar ga manema labarai, Yayar Bobo ta bayar da wani hukunci ne ga Bobo akan wata laifi da yayi bayan da suka dawo daga Masujada, shi kuma sai ya ki yin hakan.
“Bobo ya shige dakin shi ne yaje kuma ya sha SNIPER bayan da Baban sa ya kara tsananta masa bisa tsawatawar da yayan shi ta yi masa.” inji wanda ya bada bayani ga manema labarai.

“Baban Bobo yace Bobo yayi tsallen kwado ne bayan da yayar ta gabatar da laifin da yayi ga Babansu”

“Da jin hakan sai Bobo ya shige dakin shi da fushi, daga nan sai kwaram ya dauki Gamalen ya sha ba tare da sanin kowa ba”

Iyayen Bobo su gane da hakan ne bayan da gamalen ya riga ya canye hanjin sa har ga bakin mutuwa.
Duk da kokarin da akayi don ribato ran Bobo ya zaman abin banza ne a yayin da maganin ya riga ya shige shi kwarai da gaske.

A halin yanzu, bisa rahoto, Mutanen garin Aniebo ta karamar hukumar Gadumo a Jihar Kogi na cikin Kuka da kaito game da mawuyacin hali na mutuwar Bobo.

Mista Williams Aya, Kakakin yada yawun Jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar Kogi ya bayyana ga manema labarai da cewa bai karbi wata rahoto ba tukunna game da lamarin.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Hukumar Jami’an tsaron Jihar Jigawa sun gabatar da wani matashi da ya nutsa a ruwa a kauyan Shaiskawa da ke a karamar hukumar Kazaure.

SP Abdu ya bayyana da cewa Abubakar ya fada cikin DAM din ne a yayin da Hukumar Yaki da Amfani da Mugan Kwayoyi (NDLEA) ke biye da shi bayan da aka gane shi da alamun ajiyar mugan kwayoyi.