Connect with us

Uncategorized

Kannywood: Wanda yayi laifi ya kamata a yafe masa – Adam A. Zango ya roki Ali Nuhu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Ali Nuhu, Adam A. Zango

Mun Ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa mun gano da wata takardan karan Kotu da Ali Nuhu ya gabatar a kotun kara game da fadan sa da Adam A. Zango

Ko da shike ba mu iya gane ainihin dalilin fadan su ba, amma bisa ga bayanin da ke cikin takardan Kotun, an bayyana ne da cewa Adam A. Zango na kokarin bata wa Ali Nuhu suna ne.

A yau kuma mun gano da sabuwar bidiyo inda Shahararan dan shirin fim din, Adam ya shirya wata bidiyo da ya gabatar da cewa lallai lokaci yayi da za a gafarta wa juna.

A cikin bidiyon, An bayan da Adam yayi sallama, ya yi Ikirarin kansa a matsayin Sabon Shugaban tsare-tsare na kasa a shekara ta 2020.

Ya kuma ci gaba da cewa “Lallai lokaci ya kusanto da Watan Ramadan, ya kamata kuma duk wandan yayi laifi ya nemi gafara, wanda kuma aka yi wa laifi ya gafarta”

Kalli sakon Adam a kasa kamar yadda ya bayar a cikin bidiyon;

Kalli yadda aka shirya su a cikin wata bidiyo;