Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 16 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

 

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 16 ga Watan Afrilu, 2019

1. Buhari bai bukatar takardan WAEC kamin ya yi Shugabancin Kasar Najeriya – Keyamo

Kakakin yada yawun Jam’iyyar APC wajen hidimar neman zabe, Festus Keyamo (SAN) ya gabatar da cewa ba dole sao mutum na da takardan WAEC ba kamin yayi shugabancin kasar Najeriya.

Keyamo ya bayar da wannan bayanin ne a ranar Lahadi da ta gabata don mayar da martani ga wata zancen da ake na cewar, shugaba Muhammadu Buhari bai dace da takaran shugabancin kasa ba.

2. Kungiyar IPOB ne kawai zata iya kwato yancin Biafra – inji Nnamdi Kanu

Shugaban Kungiyar ‘yan Iyamirai (IPOB), Nnamdi Kanu ya yi barazanar cewa babu kungiyar da zata iya kwato yancin kasar Biafra sai dai kungiyar shi ta IPOB.

Naija News ta gane da wannan bayanin ta Kanu ne a wata gabatarwa da yayi a Gidan Radiyon Biafra, a ranar Lahadi da ta gabata.

3. Kotun CCT za ta gabatar da Shari’ar ta ga karar Onnoghen a ranar Alhamis ta gaba

Kotun Hukunci (CCT), ta bayyanar da ranar Alhamis, 18 ga watan Afrilu 2019 don gabatar da shari’ar su a kan karar da ake ga tsohon shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, akan wasu zargi shidda da ake da shi.

An gabatar da hakan ne daga bakin Ciyaman na Kotun Hukuncin, Danladi Umar, a ranar Litini da ta wuce.

4. Kotu ta saki wadanda ake zargi da kisa a Ikkilisiyar Ozubulu

Kotun Koli ta Awka, babban birnin Anambra, ta gabatar da sakin wasu mutane biyu da ake zargi da kashe mutane a wata Masujadar da ke garin Ozubulu, ta Jihar Anambra.

Naija News Hausa ta gane da cewa Kotun ta yi hakan ne bayan da ta kula da cewa zargin da ake ga Chinedu Akpunonu da kuma Onyebuchi Mbanefo bai kama kasa ba.

5. Hukumar INEC:  Atiku ne ya yi hade-haden Kuri’un da yake gabatarwa  – inji APC

Jam’iyyar da ke shugabancin kasar Najeriya, APC na zargin tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar da hade-haden kuri’u da ya banbanta da ta Hukumar INEC.

Dan takaran kujerar shugaban kasan Najeriya daga Jam’iyyar PDP ga zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar ya gabatar a baya da wata sakamakon zabe da ta banbanta da wadda Hukumar INEC ta bayar.

6. Dalilin da ya sa APC ke kalubalantan Atiku a matsayin dan Kamaru – Keyamo

Kakakin yada yawun Jam’iyyar APC ga hidimar neman zabe, Festus Keyamo ya bayyana dalilin da ya sa Jam’iyyar APC ke jayayya da Atiku game da zancen cewa Atiku ba dan kasar Najeriya ba ne.

Jam’iyyar Shugabancin kasar, APC ta gabatar ne da wata kara a gaban kotun kara da cewa Atiku Abubakar, dan takaran kujerar shugaban kasa daga Jam’iyyar PDP, dan Kamaru ne ba dan kasar Najeriya bane.

7. Zamu ba ‘yan Najeriya Mamaki akan Rahoton mu na zargin NAF da kashe Mutanen da ba ‘yan ta’adda ba

Kungiyar Manyan Sarakuna da Wakikan Jihar Zamfara sun dage da cewa lallai Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya sun kure harin da suka kai wa ‘yan ta’adda a Jihar. “maimakon kashe ‘yan ta’adda, mutanen kauyukan ne aka kashe.”

Kungiyar ta gabatar ne da hakan a wata bayani da Alhaji Hassan Attahiru, Sarkin Bungudu da kuma kakakin Kungiyar ya bayar ga manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata.

8. APC na shirin gabatar da tsarin shugabancin gidan Majalisar Dattijai

Jam’iyyar Shugabancin kasa, APC sun bayyana da cewa suna kan shirin tsarafta shugabancin gidan Majalisar Tarayya ta tara.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a wata ganawar Sakataren yada labarai ga Jam’iyyar, Lanre Issa-Onilu, yayi da manema labarai a daren ranar Lahadi da ta gabata.

9. Kotun Kara ta sake gabatar da bukatar kame Jay Jay Okocha

Kotun Koli ta Birnin Legas da ke a yankin Igbosere ta sake bayyana sabon shiri don kame tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa na Najeriya, Augustine Jay-Jay Okocha akan wata zargi.

Naija News Hausa ta gane da cewa Kotun ta yi hakan ne bisa wata zargi da ake yi da Okocha na zancen cewa yaki biyan kudin harajin sa da ya kamata yana biya kai-da-kai. Kamar yadda muka sanar a baya.

Ka samu kari da cikakken labarin Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com

Advertisement
close button