Connect with us

Uncategorized

‘Yan Hari da Makami sun Kashe mutane 16 a wajen Zanen Suna a Jihar Nasarawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jihar Nasarawa ta fuskanci wata sabuwar hari daga ‘yan hari da makami, inda aka kashe kimanin mutane 16 a wajen zanan suna.

Gidan yada labaran mu ta gane da lamarin ne a wata sanarwa da ya bayyana yadda ‘yan hari da makami suka hari Kauyan Numa da ke shiyar Andaha ta karamar Hukumar Akwanga, a ranar Lahadi da ta gabata.

Ana zargi da zaton cewa makiyaya Fulani ne suka kashe mutane 16 a harin da aka yi a kauyan Numa, ranar Lahadi da ta wuce a yayan da ake wata zanan suna.

An kuma bayyana da cewa ‘yan ta’addan su yi wa wata matashiyar yarinya fyade kamin dada suka kashe wani tsoho mai shekaru dari (100) da kuma da ya halarci wajen zanan sunan.

Sanatan da ke wakilcin Arewacin Jihar Nasarawa, Philip Gyunka ya bada tabbacin harin ga manema labarai a ganawar su a garin Akwanga. Ya bayyana da cewa cikin mutanen da aka kashe, akwai wani Magidanji da Matarsa hade da dan su.

Sanata Gyunka ya bayyana bacin ransa da hakan, ya ce “Wannan abin takaici ne, An kashe Mutum da Matarsa da dan su a hari daya. Wata Macce da ke da juna biyu ta mutu a wajen da kuma tsoho mai shekaru 100.”

“Wannan mumunar hari ne. Ba su bar babba, yaro, macce, ko jariri ba. Haka kawai suka shiga kashin mutane ba dalili.” inji Gyunka.

Karanta wannan kuma: Abdulrahman yayi Barazanar Kashe Kadaria Ahmed don janyewa daga Musulunci

“Yankin Akwanga zuwa hanyar Abuja na fuskantar hare-hare da sace-sacen mutane a kowace lokaci. Wannan sakamakon rashin bincike matafiya ne musanman masu yawo da makami.”

Ya kara bayyana da cewa yayi wata gabatarwa a gidan Majalisa na bukatar Gwamnatin Tarayya da kafa rukunin Rundanar Sojoji a garin Akwanga.

“Mun rasa kimanen mutane 16 da kuma mutane da dama da suka samu raunuka sakamakon harin. ‘Yan ta’addan sun cin ma mutanen kauyan da yin zanen suna, suka kuma fada masu da harbi” inji shi.

Ko da shike ba a samu karban bayani ba daga bakin Mista Bola Longe ba, watau Kwamanda Jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar Nasarawa, a lokacin da aka bayar da wannan rahoton harin.