Connect with us

Uncategorized

Kannywood na cikin Rudu: Amina Amal tayi karar Hadiza Gabon a Kotu da bukatan Miliyan N50m

Published

on

at

Naija News Hausa ta gano da wata rahoto da cewa Shahararriyar ‘yar shirin fim na Hausa, Amina Amal ta wallafa kara ga Kotu Koli ta Jihar Kano, a kan fadan ta da Hadiza Aliyu Gabon.

Mun ruwaito a baya da cewa Shahararrun Manya daga cikin ‘yan fim na Kannywood biyu sun shiga kafar wando guda. Watau Ali Nuhu da Adam A. Zango.

Ko da shike mun sanar kuma da baya da yadda aka shirya Shahararun, musanman wata bidiyon da ke dauke da Adam A. Zango inda ya nuno kansa da neman sulhu da Ali Nuhu. Ko da shike bai gabatar da sunan Ali Nuhu ba amma kalaman sa a cikin bidiyon ya bayyana hakan.

Yace “Lokaci yayi da ya kamata a yafe wa juna. Wanda aka yi wa laifi ya yafe, wanda kuma yayi wa wani laifi ya nemi gafartawa” inji Adam.

Shararrar ginbiya da kuma Haifafar kasar Kamarun, da aka sani a baya a matsayin kawar Hadiza Gabon, Amal ta gabatar da cewa Hadiza ta ci mutuncin ta da kuma muzurta ta, a hakan ne ta wallafa kara da bukatar Kotun Koli ta Jihar Kano da  tsananta da kuma sa Hadiza ta roke ta da kuma biyar ta kudi kimanin naira Miliyan Hamsin (N50m) hade da manyan shaidu biyu a gaban kotun.

Kalli karar a kasa;

Kalli Bidiyon Karar a nan;