Connect with us

Uncategorized

Kash!, Kalli Yadda aka yi wa wani Soja da ke kokarin ‘kare wani

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan Zanga-Zanga sun yi wa wani Sojan Najeriya mugun duuka a yayin da yake kokarin ‘kare su daga kashe wani direban babban mota da bugu.

Naija News Hausa ta gano da wannan rahoton ne kamar yadda aka bayar a wata rahoto da cewa wasu ‘yan Zanga-Zanga sun yi wa Sojan mugun bugu ne kamar zasu kashe shi. Bisa bayanin da aka bayar ga manema labarai, Sojan ya gano su ne yadda suka tarar ma wani Direban babban mota da bugu akan zargin cewa direban ya kashe wani dan uwansu da mota a shiyar Ajegunle ta Jihar Legas.

Ko da shike wadanda suka ga yadda abin ya faru sun bayyana da cewa ba da gangan bane direban ya hau dan uwan nasu da mota ba.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Wata Jirgin Kasa ta hau kan Mutane biyu a Jihar Kano a yayin da suke kokarin ketarawa.

Bisa bincike, Direban babban motar ya take dan uwan nasu mai suna Kola Mutiu ne a yayin da Kola ke kokarin karban kudi daga hannun direban.

Black Jesus, watau Kola Mutiu kenan kamar yadda aka fi sanin shi a unguwar su ya kai ga karshen rayuwan sa a karkashin babban Tirela”

Ko da shike Kola bai mutu ba anan take da motar ta take shi, amma ya karshe nunfashin sa ne ta karshe bayan ‘yan mintoci kadan da aka isar da shi a asibiti don samun kulawa.

Haushin hakan ne ‘yan uwan nasa da suke unguwa guda suka haura da bin direban Tirelan, daga isa wajen suka hau shi da bugu kamar zasu kashe shi.

“suna cikin bugun direban ne, sai ga wani Soja ya iso wajen, ya kuma fada a tsakar su da kokarin hanna su bugun direban. Da kuma suka ga hakan, sai suka hada hannu da  hawan Sojan da bugu” kamar yadda aka bada rahoto ga manema labarai.

Karanta wannan kuma; Hukumar NPOWER a jagorancin Gwamnatin Tarayya ta fara biyar ma’aikata albashin watan Maris da ta gabata.